Halin da Ake Ciki a Binciken da Majalisar Wakilai ke Yi kan Kafa Hukumar Bogi a Najeriya

Halin da Ake Ciki a Binciken da Majalisar Wakilai ke Yi kan Kafa Hukumar Bogi a Najeriya

  • Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken zargin kafa hukumar bogi ta PFIPC ya yi shiru tsawon kwanaki bakwai bayan zamansa na karshe
  • Hukumar ICPC ta kammala nata binciken tare da wanke Fadar Shugaban Kasa daga hannu a lamarin
  • Kwamitin ya ce ya gano wasu takardu da ake zargin an yi magudi da su da kuma wasu hukumomin gwamnati da aka danganta da PFIPC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kwana bakwai bayan Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai da ke binciken zargin kafa hukumar bogi (PFIPC) ya gudanar da zaman sauraron jama'a na karshe, har yanzu bai bayyana sakamako ba.

Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, dan APC daga Jihar Plateau, ya ki yin karin bayani kan halin da binciken yake ciki lokacin da aka tuntube shi ta waya, yana mai cewa yin hakan na iya kawo cikas ga tsarin binciken.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda aka kama dan bindiga yana cire kudin fansa a POS

Majalisa.
Zauren Majalisar wakilai ta kasa da ke babban birnin tarayya Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

An kammala binciken ICPC

Daily Trust ta rahoto cewa rashin bayyana sakamakon binciken na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matakin da kwamitin zai dauka, wanda kawo yanzu ya ƙi cewa komai.

Kwamitin Majalisar ya yi gum da bakinsa kan lamarin bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kammala nata binciken kan lamarin.

ICPC ta ce babu hannu daga Fadar Shugaban Kasa wajen zargin kafa hukumar bogi, kuma ta mika rahotonta ga Shugaba Bola Tinubu.

A zamansa karshe, kwamitin majalisar wakilai ya duba wasu takardu da shaidu da suka shafi hukumar da ake zargin an kafa, ciki har da bayanan hukumomin gwamnati kan yadda PFIPC ta samu karbuwa a hukumance.

Kwamitin ya gano zargin magudin takardu

A baya, kwamitin ya bayyana cewa ya gano abin da ya kira babban magudin takardu, ciki har da amfani da wasu takardun da ake ikirarin na gwamnati ne.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An tura saƙo ga Amurka da Birtaniya don su hukunta sanatan Najeriya

Kwamitin ya kuma ce an samar da wata Directorate of Administration and Support Services a karkashin Fadar Shugaban Kasa, alhali jami'an gwamnati sun ce babu irin wannan sashi a can.

Fadar Shugaban Kasa ta kuma musanta cewa ta taba bayar da wasikar nadin mukami ga Prince Adeniyi Adeyemi, wanda ake kira Darakta-Janar na PFIPC.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) kuma ta bayyana yadda wasu motocin da ake alakanta su da PFIPC suka samu lambobin motocin gwamnati, kamar yadda Punch ta kawo.

Shugaban kwamitin ya taba bayyana cewa wadannan sabani da aka gano za su kasance cikin abubuwan da kwamitin zai yi la'akari da su yayin tsara rahotonsa na karshe.

Har yanzu babu rahoton karshe

Sai dai duk da alkawarin da kwamitin ya yi na kammala binciken tare da sanar da 'yan Najeriya sakamakonsa, har yanzu babu wata sanarwa daga kwamitin bayan shafe kwanaki bakwai.

Har ila yau, kwamitin ya bayyana a baya cewa zai gana da Adeyemi, wanda ke tsare, a wani lokaci da kuma wurin da ba a bayyana ba, maimakon gudanar da zaman a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Ana shirin binciken Adeyemi, shugaban PFIPC na bogi ya roki alfarmar majalisa

Shugaban bogi.
Shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a kanta, Prince Adeniyi Adeyemi Hoto: Adewale John
Source: Facebook

Ana sa ran rahoton karshe na kwamitin zai yi karin haske kan yadda PFIPC ta gudanar da ayyukanta, rawar da hukumomin gwamnati suka taka, da ko jami'an gwamnati ko wasu mutane masu zaman kansu ne suka taimaka wajen gudanar da ayyukanta.

Adeyemi ya yi tone-tone kan PFIPC

An ji cewa Adeniyi Adeyemi, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban hukumar PFIPC ya musanta zargin cewa shi kaɗai ya ƙirƙiri hukumar da ake takaddama a kanta.

Adeyemi ya ce ma’aikatu da hukumomi daban-daban na gwamnatin tarayya sun gudanar da ayyuka, sun amince ko kuma sun yi hulɗa da hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262