Kiristoci Sun Samu Dama a Shirin Auren Gata da Gwamna Abba Zai Ƙara Yi a Kano
- Gwamnatin Kano ta bude koga ga kiristoci domin su amfana da shirin auren gata da ta saba gudanarwa domin tallafawa masu karamin karfi
- Hukumar Hisbah ta bayyana cewa kiristoci sun amfana da auren gata a baya, kuma har yanzu kofa a bude matukar suka cika sharudda
- Gwamnatin Kano ta fi mayar da hankali wajen taimaka wa marayu da iyalan marasa galihu da ba su da karfin daukar nauyin auren 'ya'yansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa shirin auren gata da gwamnatin jihar ke daukar nauyi a bude yake ga Musulmi da Kiristoci matukar sun cika sharudda.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Kano, inda ya yi karin haske kan ka'idojin shiga shirin.

Source: Facebook
An ba kiristoci damar shiga auren gata
Ya bayyana cewa ma'aurata Kiristoci uku sun samu shiga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin auren gata da aka gudanar a watan Oktoban 2023, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Ya ce duk da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen sabon zagayen shirin, har yanzu ba za a iya tabbatar da ko akwai wasu ma'auratan Kirista da suka yi rajista ba.
Aminuddeen ya ce shirin, wanda yanzu ake kira auren gata, an tsara shi ne domin zawarawa, mazajen da suka rasa matansu, wadanda aka raba aure, 'yan mata da samari da ba su taba yin aure ba.
Dalilin samar da shirin auren gata a Kano
A cewarsa, shirin na taimakawa wajen gina zaman lafiyar iyali tare da rage ayyukan da suka saba wa tarbiyyar addini a cikin al'umma.
Ya kara da cewa daya daga cikin manufofin shirin ita ce aiwatar da umarnin Annabi Muhammad (SAW) na karfafa yin aure da kafa iyali, cewar rahoton Punch.
Ya ce shirin na kuma rage yawon talla da wasu 'yan mata ke yi domin tara kudin aure, tare da dakile dabi'un da ba su dace ba da ke faruwa sakamakon jinkirin aure saboda matsalolin tattalin arziki.
Mataimakin kwamandan ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fi mayar da hankali wajen taimaka wa marayu da iyalan marasa galihu da ba su da karfin daukar nauyin auren 'ya'yansu mata.
Masu ruwa da tsaki sun yabawa shirin
Wani malamin addini, Sheikh Muhammad Lawan-Yakub, ya bayyana shirin a matsayin kyakkyawan mataki da zai taimaka wajen karfafa zaman iyali, rage lalacewar tarbiyya da inganta zaman lafiya a cikin al'umma.
Ya ce horaswa, shawarwari da kulawar da Hisbah ke bai wa ma'aurata kafin da bayan aure za su taimaka wajen samun zaman aure mai dorewa tare da rage yawan rabuwar aure.

Source: Facebook
Ita ma wata mazauniyar Kano, Jamila Surajo, ta ce shirin ya taimaka wa iyalai da dama mqqqasu karamin karfi, tare da yin kira ga masu son shiga shirin su yi aure da kyakkyawar niyya.
Sai dai ta nuna damuwa cewa wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin a baya sun shiga ne saboda tallafin gwamnati ba wai don gina zaman aure mai dorewa ba.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ndume ya gano matsalar da Tinubu ke fuskanta a fadar shugaban kasa
Gwamnatin Kano ta ware kudin auren gata
A baya, an ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware Naira biliyan 1.5 domin gudanar da auren gata.
Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano , Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa domin gudanar da auren ma'aurata 1,500.
Sheikh Daurawa ya ce ɓangare na shirye-shiryen ya ƙunshi gwaje- gwajen lafiya na kafin aure kamar su kwayar cutar kanjamau (HIV), cutar hanta, juna biyu, da kuma gwajin nau'in jini.
Asali: Legit.ng

