Za a Yi Auren Gata a Kano, 'Yan Mata, Zawarawa da Samari 3,000 za Su Angwance

Za a Yi Auren Gata a Kano, 'Yan Mata, Zawarawa da Samari 3,000 za Su Angwance

  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Kano, karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta shirya gudanar da auren gata a jihar a 2026
  • Shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da cewa mutane 3,000 gwamnatin Abba za ta aurar
  • Sheikh Aminu Daurawa ya kuma bayyana abubuwan alheri da gwamnatin Kano ta tanada domin tabbatar da an yi hidimar auren lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta fara shirye-shiryen gudanar da auren gata ga dubban mata da maza a jihar a shekarar 2026 da muke ciki.

A wani bayani da hukumar Hisbah ta yi, ta nuna cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai dauki nauyin abubuwan da za a kashe yayin bikin.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yi martani ga Gwarzo, ya fadi abin da zai hana Abba faduwa zabe a Kano

Yadda aka yi auren gata a Kano
Wajen daurin auren gata a Kano a 2023. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da daurin auren ne a wani sako da shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Mutanen da za a aurar a Kano

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta aurar da zawarawa da ’yan mata guda 3,000 (maza 1,500 da mata 1,500).

Game da wadanda za su amfana da shirin, shugaban hukumar Hisbah ya ce:

"Mafi yawan waɗanda za su amfana da wannan shiri marayu ne da kuma ’ya’yan talakawa."

Kayayyakin da aka tanada

Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta tanadi kayan daki da duk abubuwan da ake bukata wajen daura auren.

Ya ce abubuwan da aka tanada masu sun haɗa da:

1. Kayan ɗaki (gado, madubi, katifa, filo da zanin gado).

2. Kayan abinci (shinkafa, taliya da jarkar mai).

3. Atamfa da hijabi ga mata.

Kara karanta wannan

Gwarzo: "Adadin Kanawa da ake hallakawa a gwamnatin Abba ya fara yawa"

4. Shadda da hula ga maza.

5. Sadaki na N00,000 ga kowace amarya.

6. Jarin N100,000 ga kowace amarya domin fara sana’a.

Kayan aure da aka saya a Kano
Wani sashe na kayan auren gata da gwamnatin Kano ta saya a 2023. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Za a masu gwajin lafiya

Yayin da yake bayani game da tabbatar da lafiyar wadanda za a aurar, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa likitoci za su tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya.

Ya ce:

"Haka kuma za a gudanar da gwaje-gwajen lafiya tare da cike fom uku domin tabbatar da cewa kowa ya cika sharuɗɗan shiga wannan shiri."

Ya rufe bayan shi da cewa:

"Muna roƙon Allah maɗaukakin sarki ya saka wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da alkhairi, ya sanya albarka a wannan aiki na tallafawa marayu da ’ya’yan talakawa, Ya kuma sanya a samar da gidajen aure masu cike da zaman lafiya, soyayya da albarka. Amin."

Hisbah ta kai samame otel

A wani labarin, kun ji cewa jami'an hukumar Hisbah ta jihar Sokoto sun kai samame wasu otel-otel da ake zargi ana badala a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Hukumar ta sanar da cewa a otel guda uku da ta kai farmaki, ta yi nasarar cafke maza da mata sama da mutum 10 da ake zargi da aikata ba daidai ba.

Mukaddashin shugaban kungiyar a jihar Sokoto ya yi karin bayani da cewa an kaddamar da samamen ne a karkashin Operation Tsaftace Birnin Shehu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng