Kwankwasiyya Ta Shiga Batun Ma'aikatar Bogi, Ta Aika Sako ga Gwamnatin Tinubu

Kwankwasiyya Ta Shiga Batun Ma'aikatar Bogi, Ta Aika Sako ga Gwamnatin Tinubu

  • Batun ma'aikatar bogi da ake zargin an kafa har ta yi aiki na ci gaba da jawo cece-kuce-kuce a tarayyar Najeriya
  • Gwamnatin tarayya a na ta bangaren ta bayyana cewa ba ta san da zaman ma'aikatar ba duk da shakkun da wasu ke yi
  • Kungiyar Kwankwasiyya ta fito ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiya kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci a gudanar da cikakken bincike kan takaddamar da ta shafi zargin wanzuwar hukumar PFIPC.

Kwankwasiyya ta bayyana cewa lamarin ya wuce matakin abin da mutum guda ya aikata, kuma a yanzu ya tayar da muhimman tambayoyi game da gwamnati.

Kwankwasiyya ta yi magana kan ma'aikatar bogi
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya fitar a ranar Asabar, 4 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Umarnin da fadar shugaban kasa ta ba DSS, EFCC kan batun ma'aikatar bogi

Me Kwankwasiyya ta ce kan ma'aikatar bogi?

Kwankwasiyya ta bayyana takaddamar da ke ci gaba da faruwa a matsayin “babban gwaji ga sahihanci, gaskiya, da rikon amana na gwamnatin tarayya.”, jaridar TheCable ta kawo rahoton.

Kungiyar ta lura cewa ko da yake fadar shugaban kasa ta musanta wanzuwar PFIPC tare da nesanta kanta da mutanen da ke da'awar wakiltar hukumar, rahotannin cewa an ware fiye da N1bn a cikin kasafin kudin 2026 don wata hukuma mai dauke da suna iri daya ko makamancin haka, na bukatar cikakken bayani ga jama'a.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Wannan takaddama ba za a iya yin watsi da ita kawai a matsayin ba daidai ba na mutum guda ba. 'Yan Najeriya suna da hakkin su sani” yadda hukumar da Fadar Shugaban Kasa ta ce ba ta taba wanzuwa ba ta shiga cikin kasafin kudin kasa."
"Wanda ya gabatar da kudirin kudin da kuma amincewa kudin, wadanne ofisoshin gwamnati ne suka sarrafa takardun, ko an fitar da wani kudin gwamnati, da kuma yadda aka yi amfani da takardun gwamnati da ake zargin na jabu ne “na tsawon lokaci ba tare da an gano su ba.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya

Kwankwasiyya ta ce ba siyasa ba ce

Kungiyar ta jaddada cewa batutuwan da aka tayar sun wuce batun siyasa, tana mai cewa sun shafi yadda ake tafiyar da arzikin kasa ne.

“Wadannan ba tambayoyi ne na bangaranci ba. Tambayoyi ne na rikon amana na jama'a,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wadda ta hau karagar mulki a kan alkawuran sabunta fata, gyaran hukumomi, da shugabanci na gari, ya kamata ta nuna sadaukarwarta ga wadancan alkawuran ta hanyar bayar da cikakken bayani kan lamarin.

Kwankwasiyya na son a yi bincike kan ma'aikatar bogi
Adeniyi Adeyemi da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Wace bukata ta mika ga gwamnati?

Don haka, kungiyar ta bukaci fadar shugaban kasa da ta “wallafa cikakken bayani na gaskiya, gami da asalin tanadin kasafin kudin, hanyoyin gudanarwa da abin ya shafa, da kuma matakan da ake dauka don hana afkuwar hakan nan gaba.”

Ta kuma yi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa, hukumomin yaki da rashawa, da sauran hukumomin sanya ido da su gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin daidai da doka.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Atiku ya tsoma baki, ya ba Tinubu wa'adi don gano gaskiya

Za a yi bincike kan ma'aikatar bogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa za a gudanar da bincike kan takaddamar ma'aikatar bogi.

Fadar shugaban kasa ta umarci DSS, EFCC da su zakulo mutanen da ke cikin gwamnati da ke aiki tare da Adeniyi Adeyemi don gudanar da hukumar PFIPC domin a gurfanar da su.

Ta yi zargin cewa akwai masu haɗin baki na cikin gida da ke ba Adeniyi damar yin kamfen ɗin ɓata suna da ake yi wa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com