Harin Borno: Adadin Daliban da Ake Nema yanzu Ya Haura 30, Kansila Ya Yi Bayani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Akalla dalibai 35 ne har yanzu ake nema bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare da ke Lassa, karamar hukumar Askira/Uba
- Wata kansilar yankin ta ce an kubutar da dalibai bakwai da malami guda, yayin da ake tattara sunayen wadanda ba a gani ba tun bayan wannan hari
- Rundunar soji ta ce ta kubutar da mutane 10 bayan arangama da maharan, amma ana ci gaba da aikin bincike a dazuzzuka da sassan yankin
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Borno - Akalla dalibai 35 ne har yanzu ba a gano inda suke ba bayan ‘yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare da ke Lassa, karamar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.
Kansilar da ke wakiltar Lassa Ward, Jagila Jabila, ce ta bayyana hakan, tana mai cewa jami’an tsaro da al’ummar yankin na ci gaba da aikin bincike domin gano daliban.

Source: Getty Images
Dalibai 35 sun bace a harin Borno
A zantawar ta da jaridar Premium Times, Jabila ta musanta rahotannin da suka yadu a kafafen sada zumunta cewa an kubutar da dukkan daliban da aka sace.
Ta ce:
“Wannan ba gaskiya ba ne.
“An samu nasarar kubutar da dalibai bakwai ne da malami guda. Yanzu muna tare da iyayensu, muna tattara sunayen daliban da suka bata. Zuwa yanzu muna da sunaye 35 da suka bace.”
Ta bayyana cewa adadin ya samo asali ne daga bayanan iyaye da shugabannin al’umma, kuma yana iya canzawa yayin da ake kara tantance bayanai.
Badda kama da 'yan ta'adda suka yi
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Nahum Daso, ya ce maharan sun yi amfani da ranar kasuwar garin domin shiga yankin cikin sauki.
Da yake magana a shirin The Morning Show na Channels TV, ya ce maharan sun boye makamansu tare da sajewa da ‘yan kasuwa.
Kakakin 'yan sandan ya ce:
“Yan bindigar sun shiga garin Lassa a ranar kasuwa, suka saje da ‘yan kasuwar, suka boye makamansu, suka shiga garin sannan suka fara harbe-harbe."
Da aka tambayi Jabila kan rahotannin cewa maharan sun sanya kayan sojoji da jami’an tsaron daji domin batar da mutane, ta ce hakan gaskiya ne.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kashe malami guda a harin, yayin da wani malami ya samu raunin harbin bindiga.

Source: Original
Ana ci gaba da tantance wadanda suka bace
Jami’an tsaro sun ce har yanzu ana kokarin gano hakikanin adadin wadanda abin ya shafa, saboda wasu dalibai sun tsere zuwa kauyukan da ke kusa bayan harin.
Daso ya ce ana hada bayanan halartar makaranta da bayanan iyaye domin tantance yawan daliban da har yanzu ba a gano su ba.
Sojoji sun ceto wasu yaran
Tun da fari, mun ruwaito cewa, dakarun ‘Operation Hadi Kai (OPHK) sun ceto ɗalibai masu rubuta jarabawar NECO da malamai guda 10 da aka sace a Borno.
Daliban da malaman da sojoji suka ceto na daga cikin waɗanda ake zargi 'yan ta'addan ISWAP ne suka yi garkuwa da su lokacin wani hari da suka kai garin Lassa da ke Askira/Uba.
Yayin bin sawun, dakarun sojoji sun kuma ƙwato babura guda bakwai mallakin 'yan ta'addan, lamarin da ya kawo babban cikas ga zirga-zirga da tserewarsu.
Asali: Legit.ng


