Bidiyo: Majalisar Shura Ta Kano Ta Yi Zama da Sheikh Lawan Triumph a Ofishin DSS

Bidiyo: Majalisar Shura Ta Kano Ta Yi Zama da Sheikh Lawan Triumph a Ofishin DSS

  • Kwamishin Shura na jihar Kano ya yi zama da fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Lawan Abubakar watauu Triumph a ofishin DSS
  • An ce kwamitin ya yi wa malamin tambayoyi game da zargin batanci ga Annabi da ake yi masa, inda shi kuma ya kare kansa
  • A bidiyon da Legit Hausa ta samu, an ji Sheikh Triumph ya shaida wa kwamitin cewa kofarsa a bude take idan aka ga ya yi kuskure

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi zama tsakanin Sheikh Lawan Triumph da wakilai daga kwamitin Shura, jihar Kano.

An yi wannan muhimmin zaman ne a wani kebantaccen wuri a ofishin hukumar DSS, inda ake sa ran malam zai kare kalamansa.

Majalisar Shura ta Kano ta yi zama da Sheikh Lawan Triump a ofishin DSS
Hoton Sheikh Lawan Triumph yana jawabi gaban kwamitin Shura a ofishin DSS a Kano. Hoto: Qs Ibraheem Sagir Zaria
Source: Facebook

Majalisar Shura ta yi zama da Sheikh Triumph

Kara karanta wannan

An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu

Jaridar Aminiya, ta rahoto cewa, an gudanar da wannan taron ne a sirri, kuma za a yi wa Sheikh Triumph tambayoyi kan zarginsa da batanci ga Annabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga 'yan kwamitin Shura, rahoto ya nuna cewa Wazirin Kano, Shehu Gidado, da daraktan DSS da wasu manyan malamai sun halarci zaman.

Wani karamin kwamiti da majalisar Shurah ta kafa ne ya yi zama da malamin.

An rahoto cewa an fara wannan zaman ne tun da misalin ƙarfe 11:39 na safe, inda Malam Lawan Triumph ya yi ƙarin haske kan maganganun da ake zarginsa da su.

An ce taron ya kuma samu halartar wakilai daga kungiyoyi daban daban, da 'yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren addini a Kano.

Wani bangare na kalaman Sheikh Triumph

Gidan rediyon Freedom na Kano ya wallafa bidiyo a shafinsa na Facebook, inda aka nuna Sheikh Lawan Triumph yana jawabi.

Sheikh Lawan Triumph ya tashi gaban kwamitin Shura, inda ya bayyana cewa:

"Duk mai hankali da tunani idan an yi masa nasiha, to ba ya daukar wanda ya yi masa nasiha a matsayin makiyi, yana daukarsa a matsayin masoyi."

Kara karanta wannan

Donald Trump ya tafi asibiti duba lafiyarsa, Amurkawa na jefa tambayoyi

Malamin ya ce mutum kan dauki nasiha ko da kuwa wanda ya yi nasihar ya yi ta ne da wata manufa, yana mai cewa, amfanin nasiha shi ne gyara kayanka.

"Da wannan nake godiya ga wadannan iyaye na al'umma baki daya, tun daga kan ita gwamnatin jihar, har zuwa iyayenmu baki daya, har ita kanta kwamitin Shura."

- Sheikh Lawan Triumph.

Sheikh Lawan Triumph ya ce kofarsa a bude take idan aka ga ya yi kuskure a karantarwarsa
Hoton Sheikh Lawan Triumph yana jawabi gaban kwamitin Shura a ofishin DSS a Kano. Hoto: Qs Ibraheem Sagir Zaria
Source: Facebook

"Kofarmu a bude take" - Triumph ga Shura

Malamin Izalar ya shaida wa kwamitin Shura cewa kofarsa a bude take a kowane lokaci na karbar gyara daga 'yan kwamitin, yana mai cewa:

"Kofarmu a bude take, musamman ma ni. A duk lokacin da aka ga wani abu ba dai dai ba wanda na yi, to za a iya kira na.
"Kuma duk wanda ya sanni, ya san zan iya tako wa inje gidan kowane malami, a matsayin gidana ne, gidanmu ne, domin inji nasiha ko fadakarwa.

Sheikh Triumph ya kuma yi addu'a a kan Allah ya hada kan malamai, ya kuma yi wa shugabanni jagora, yayin da ya yi sallama da kwamitin.

A shafinsa na Facebook, malamin ya rubuta 'Alhamdulillah' har sau uku, wanda wasu ke ganin alama ce ta an kammala wannan zama cikin nasara.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Sai dai, har yanzu ba a wani samu cikakken bayani game da tambayoyin da malamin ya amsa ba, da kuma yadda ya kare kansa gaban kwamitin.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Bala Lau ya goyi bayan Sheikh Triump

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sheikh Bala Lau ya ce Ahlussunnah ne ke kare martabar Manzon Allah (S.A.W) tare da bin koyarwar Alƙur’ani da Hadisai.

Malamin ya jaddada cewa Sheikh Lawan Triumph yana faɗakar da Musulmai kan haɗarin jingina abubuwan da ba su da hujja ga Manzon Allah (S.A.W).

Shugaban kungiyar na JIBWIS ya gargadi gwamnati da kada ta tsoma siyasa cikin binciken da ake yi kan muhawarar Triumph da wasu malamai a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com