An Sa Mata Sun Yi Tsirara da Wasu Sojoji Suka Kai Samame Dakunan Dalibai a Jami'ar UNIOSUN

An Sa Mata Sun Yi Tsirara da Wasu Sojoji Suka Kai Samame Dakunan Dalibai a Jami'ar UNIOSUN

  • Jami'ar jihar Osun (UNIOSUN) ta tabbatar da cewa wasu dakarun sojojin Najeriya sun kai samame ɗakin kwanan dalibai da daddare
  • Hukumar jami'ar ta bayyana yadda sojojin suka ci zarafin dalibai mata ya hanyar sanya su cire kayan jikinsu, tare taɓa su
  • Mai magana da yawun jami'ar UNIOSUN, Ademola Adesoji, ya ce sama da dalibai 20 sun tabbatar da cewa abin ya shafe su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Ana zargin wasu dakaru daga sansanin horar da sojoji na Army Depot da ke Osogbo sun kai samame dakunan kwanan daliban Jami'ar Jihar Osun (UNIOSUN).

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin da ake zargi da kai wannan samame, sun kwace wayoyin hannu da sauran kayayyakin dalibai.

UNIOSUN.
Babbar kofar shiga jami'ar jihar Osun (UNIOSUN) da ke Osogbo Hoto: UNIOSUN
Source: UGC

Mahukuntan jami'ar sun ce lamarin ya faru ne a daren Litinin, kuma an kai rahotonsa ga shugabannin sansanin sojojin domin gudanar da bincike, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abubuwan fashewa sun tashi da sojan Isra'ila a Lebanon

UNIOSUN ta tabbatar da lamarin

Shugaban jami'ar UNIOSUN, Farfesa Clement Adeboye, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya kai ziyara dakunan kwanan da abin ya shafa a ranar Talata.

Ya ce abin takaici ne yadda sansanin sojin da ke kusa da jami'ar, wanda suke ganin zai taimaka wajen samar da tsaro, ya kasance tushen wannan zargin cin zarafin dalibai.

Ya ce:

"Mun kai rahoto ga mahukunta. Abin takaici ne cewa sansanin sojin da ke kusa da jami'armu, wanda muka dauka zai samar mana da kariya, ya zama inda aka fito aka yi wa dalibanmu irin wannan cin zarafi."

An zargi sojoji da cin zarafin dalibai

Mai magana da yawun jami'ar, Ademola Adesoji, ya ce sama da dalibai 20 sun tabbatar da cewa abin ya shafe su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma yi zargin cewa wasu dalibai mata sun ce jami'an sojin sun tilasta musu cire kayansu tare da taba su ta hanyar da ba ta dace ba.

Kara karanta wannan

El Rufa'i: Dalilin kotu na ci gaba da fatali da bukatar belin tsohon gwamnan Kaduna

A cewarsa:

"Mun gano fiye da mutum 20 da abin ya shafa. Sojojin sun fito ne daga sansaninsu na Osogbo kuma sun ci zarafin daliban."
"Wasu dalibai mata sun ce an tilasta musu cire kayansu, sannan aka taba su ta hanyar da ba ta dace ba. Haka kuma wasu dalibai maza sun fuskanci duka da cin zarafi."

An kwace wayoyi sama da 60

Adesoji ya bayyana cewa dalibai biyu sun samu raunuka har aka kwantar da su a asibiti, yayin da aka sallami daya daga cikinsu a safiyar Talata.

Mai magana da yawun jami'ar ya ce an kwace wayoyin hannu da kwamfutoci sama da 60 daga hannun daliban.

A cewarsa, an gano mutum biyar daga cikin wadanda ake zargi kuma an kawo su harabar jami'ar a safiyar Talata, amma daga bisani aka mayar da su sansanin soja.

Kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262