Gwamna Ya Gaji, Ya Fadi Inda Zai Rataye Masu Garkuwa da Mutane a cikin Birni

Gwamna Ya Gaji, Ya Fadi Inda Zai Rataye Masu Garkuwa da Mutane a cikin Birni

  • Gwamnan Edo Monday Okpebholo ya nuna damuwa game da karuwar laifuffukan asu garkuwa da mutane a jihar
  • Ya ce za a kafa kotu ta musamman domin gaggauta shari’a da aiwatar da hukunci a fili don tsoratar da masu aikata laifi
  • Okpebholo ya ce gwamnati tana aiki tare da ‘yan sanda, soja da DSS domin kawo ƙarshen ta’addanci da tabbatar da tsaro a Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi barazana ga masu da garkuwa da mutane a jihar.

Gwamna ya bayyana cewa za a aiwatar da hukuncin kisa a fili kan waɗanda aka samu da laifin garkuwa da mutane da ‘yan daba bayan an yanke musu hukunci a jihar.

Gwamna zai kafa dokar rataye masu garkuwa da mutane
Gwamna Monday Okpebholo na jawabi ga al'ummar Edo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da ‘yan jarida a lokacin da aka gabatar da wasu da ake zargi da garkuwa da mutane da rundunar ‘yan sanda ta kama, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An rushe katafaren gidan kasurgumin mai garkuwa da mutane da aka cafke a Edo

Gwamna zai kafa kotun masu garkuwa da mutane

Ya ce gwamnatinsa za ta kafa kotu ta musamman domin shari’ar masu laifi cikin gaggawa, sannan kuma a aiwatar da hukuncin kisa a fili domin zama izina ga wasu.

Ya ƙara da cewa ya kamata jama’a su guji shiga harkar daba da garkuwa da mutane domin hakan ba zai kai su ko’ina ba.

Ya ce:

“Ba wasa mu ke ba. Muna aiki dare da rana domin tabbatar da wannan ƙasa ta kasance lafiya.”
“Yanzu za mu kafa kotu ta musamman domin shari’ar masu garkuwa da mutane da ‘yan daba. A cikin makonni biyu zuwa uku za mu kammala. Zan kuma rattaba hannu a kai.”
“Game da hukuncin kisa da rataya, zan kai ku filin shataletale na 'Ring Road' domin duk mutanen Edo su gani. Ba zan yi nadama ba.”
Gwamna ya yi barazanar rataye masu garkuwa da mutane
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Source: Twitter

Umarnin da Gwamnan Edo ya ba yan sanda

Gwamnan ya kuma bayyana wani lamarin garkuwa da mutane da ya faru a kasuwa a babban birnin jihar a karshe makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Kotu a Kano ta yanke wa wata mata hukunci kan safarar makamai ga 'yan bindiga

Ya ce nan take ya tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar tare da umartar a kama duk masu hannu a lamarin, cewar Punch.

A cewarsa, kwamishinan ‘yan sandan da ke Abuja a lokacin ya dawo Benin City nan take, inda ya jagoranci aikin da ya kai ga kama wasu daga cikin wadanda ake zargi.

Daga baya jami’an tsaro sun bi sawun masu laifin zuwa maboyarsu, inda aka kashe ɗaya a musayar wuta, aka kama ɗaya, yayin da wasu biyu suka tsere.

Gwamnan ya yaba wa ‘yan sanda, sojoji da DSS bisa ƙoƙarinsu wajen yaki da rashin tsaro a jihar.

'Yan sanda sun bindige yan bindiga

Mun ba ku labarin cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya a ta kashe wani da ake zargi mai garkuwa da mutane ne tare da kama wani da ake zato yana satar mutane a Edo.

Rahoto ya nuna cewa an ƙwato mota, bindiga, harsasai biyu da tsabar kudi Naira miliyan 2.25 da kuma babur daga wajen wana aka kama.

Biyo bayan lamarin, Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya bayyana shirin kafa kotu ta musamman domin shari'ar masu garkuwa da mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.