Kotun Najeriya Ta Yanke wa Ibrahim da Abdullahi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Kotun Najeriya Ta Yanke wa Ibrahim da Abdullahi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

  • Babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin sace wata ma'aikaciyar NYSC a 2022
  • Alkalin kotun ya yabawa DSS saboda kwazonsu na tantance wadanda ake zargi da kuma amfani da hikima wajen tabbatar da laifin masu garkuwa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata babbar kotu a Sokoto ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa a wata shari'ar da DSS ta shigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ekiti – Wata babbar kotun jihar Ekiti ta yanke wa wasu mutum biyu, Ibrahim Abubakar da Abdullahi Abubakar, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin ne bayan samunsu da laifin sace wata ma'aikaciyar hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC.)

Kara karanta wannan

Rajistar NDC: Takarar Obi da Kwankwaso ta gamu da koma baya da kotu ta yanke hukunci

Kotu ta yanke wa mutum 2 hukuncin kisa kan garkuwa da mutane
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Yadda aka sace ma'aikaciyar NYSC

Kotun da ke zamanta a Fajuyi, Ado-Ekiti, ta yanke hukuncin ne a shari'ar mai lamba HAD/124C/2022 kamar yadda rahoton ThisDay ya nuna.

Sai dai kotun ta wanke mutum na uku, Usman Abubakar, bayan ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun gaza tabbatar da cewa yana da hannu a aikata laifin.

Shari'ar ta samo asali ne daga sace Omoboade Adesina, wata ma'aikaciyar NYSC a jihar Ekiti, wanda abin ya faru ranar 22 ga Afrilu, 2022.

Bayan gudanar da bincike mai zurfi, jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun cafke wadanda ake zargin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Kotun ta yaba wa hukumar DSS

Babban Alkalin Jihar Ekiti, Mai Shari'a Lekan Ogunmoye, ya samu Ibrahim Abubakar da Abdullahi Abubakar da laifi tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Sai dai ya wanke Usman Abubakar saboda rashin isassun hujjojin da suka tabbatar da hannunsa a aikata laifin ba tare da wata shakka ba.

Kara karanta wannan

Yadda matar Janar Rabe ta ki tafiya ta bar shi a daji duk da barazanar 'yan bindiga

Alkalin ya yabawa lauyoyin DSS bisa kwarewa da jajircewar da suka nuna wajen gabatar da shari'ar, yana mai cewa sun tabbatar da laifin wadanda aka yankewa hukunci fiye da yadda doka ta tanada.

Ya ce tantance wadanda ake zargi da aka gudanar da kuma amfani da bayanan kiraye-kirayen waya sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da laifin masu garkuwar, in ji rahoton Punch.

Kotu ta yabawa jami'an EFCC bisa bincike da yadda suka gurfanar da wadanda ake zargin.
Taswirar jihar Ekiti, inda kotu ta yanke wa mutum 2 hukuncin kisa kan garkuwa da mutane. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Nasarorin DSS a yakar masu garku

Hukuncin na daga cikin nasarorin da DSS ke samu a kokarinta na yaki da garkuwa da mutane, ta'addanci da sauran manyan laifukan da suka shafi tashin hankali a Najeriya.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata babbar kotu a jihar Sokoto ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa saboda laifukan da suka shafi ta'addanci da safarar makamai ta kan iyaka a wata shari'ar da DSS ta gurfanar.

Hakazalika, hukumar ta samu wasu nasarori a baya-bayan nan wajen tabbatar da hukuncin masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata manyan laifuka a jihohi daban-daban, ciki har da jihar Kogi.

An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa

A wani labari, mun ruwaito cewa, kotu ta yankewa mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin fashi da makami a wani kamfanin iskar gas.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Uche Onu, Ekene Okorie da Celestine Eze, wadanda aka same su da laifin fashi da makami.

Kotun ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun kawo kwararan hujjoji da suka tabbatar da laifin, don haka ya bada umarni a rataye su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com