Yadda 'Yan Ta'addan ISWAP Suka Yi Basaja wajen Sace Dalibai a Borno

Yadda 'Yan Ta'addan ISWAP Suka Yi Basaja wajen Sace Dalibai a Borno

  • 'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun kutsa wata makarantar sakandare a Borno inda suka sace daliban da ke rubuta jarabawar NECO
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno. Nahum Daso, ya bada bayanai kan yadda 'yan ta'addan suka sace daliban
  • Nahum Daso ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun badda kama ne a lokacin da ake cin kasuwar garin da aka sace daliban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sandan jihar Borno, Nahum Daso, ya yi magana kan sace daliban da 'yan ta'addan ISWAP suka yi.

Nahum Daso ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun badda kama ne a matsayin 'yan kasuwa masu sayar da kayayyaki a ranar kasuwar garin kafin su afka wa al'ummar domin yin garkuwa da ɗaliban.

'Yan ta'addan ISWAP sun sace dalibai a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Nahum Daso ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a shirin "The Morning Show" na gidan talabijin na Channels Tv a ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC

Yadda aka sace daliban

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ba da ƙarin haske kan yadda 'yan ta'addan suka samu damar shiga cikin makarantar domin yin awon gaba da ɗaliban.

“Lamarin jiya da ya auku a Borno abin takaici ne ƙwarai, wanda da gaske ya tayar da damuwa, musamman ma duba da cewa mutanen da abun ya ritsa da su ɗalibai ne."
“Abin da ya faru shi ne, a safiyar Litinin, adadi mai yawa na 'yan ta'adda sun afkawa garin Lassa. Jiya ita ce ranar kasuwa, sai suka badda kama tare da ɓoye makamansu, suka shige cikin garin sannan suka fara harbi ba kakkautawa a sararin sama.”

- Nahum Daso

'Yan ta'adda sun kashe malami

Ya bayyana cewa lamarin ya kai ga mutuwar malami guda ɗaya, yayin da wani na daban ya samu raunin harbin bindiga.

A cewarsa, kodayake dakarun sojoji sun samu nasarar ceto mutane 10 daga cikin waɗanda aka sace, wasu daga cikin ɗaliban har yanzu ba a gano inda suke ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Borno bayan ritsa 'yan ta'addan ISWAP cikin daji

“Lamarin ya kai ga mutuwar malami guda ɗaya, kuma an harbi wani malamin na daban. Mun samu rahoton cewa wasu ɗalibai sun firgita kuma sun ɓace lokacin da lamarin ke faruwa."
“Amma dakarun rundunar Hadin Kai masu ayyukan soji a nan jihar Borno sun samu damar shiga cikin dajin kuma sun binciki gurin sosai. Sun samu nasarar ceto kusan mutane 10 da abun ya ritsa da su.”

- Nahum Daso

An ceto wasu daga cikin daliban da aka sace a Borno
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno, Nahum Daso Hoto: Nahum Daso Kenneth
Source: Facebook

Dalibai nawa 'yan ISWAP suka sace?

Ya lura cewa har yanzu ba a ƙayyade takamaiman adadin ɗaliban da 'yan ta'addan suka sace ba.

“Dangane da bayanai na farko, ba mu da takamaiman adadin mutane nawa ne aka sace saboda wasu ɗaliban sun tsere zuwa garuruwan da ke maƙwabtaka."
“Muna fatan samun ƙarin bayanai a yau domin sanar da jama'a. Har yanzu ba mu daidaita adadin ba tare da makarantar da kuma iyaye. Muna da tabbacin cewa mutane 10 ne aka ceto zuwa yanzu.”

- Nahum Daso

Ndume ya aika sako ga gwamnati kan sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya yi magana kan sace daliban da 'yan ta'addan ISWAP suka yi a jihar Borno.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa makaranta a Borno, an sace daliban da ke jarabawa

Sanata Ndume ya ce sace daliban da ke rubuta NECO a jihar Borno ya nuna cewa gwamnatin tarayya na bukatar kara kokari wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Ya bayyana harin a matsayin abin takaici, yana mai cewa ya faru ne a lokacin da har yanzu ba a san makomar wasu yaran da aka sace a baya ba. Ya ce: Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng