El Rufa'i: Dalilin Kotu na Ci Gaba da Fatali da Bukatar Belin Tsohon Gwamnan Kaduna
- Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayyana rashin gamsuwa da bukatar da tsohon gwamna Nasir El-Rufai, ya gabatar a gabanta na neman beli
- Sai dai Mai shari'a Justice Diruis Khobo ya umarci ICPC ta ba El-Rufai damar samun kulawar likitocinsa ko asibitin da ya zaɓa yayin da yake tsare
- An dage shari'ar da ake yi da tsohon gwamnan Kaduna wanda ya danganci cin zarafin ofis da wadansu laifuffukan da suka danganci hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ƙi amincewa da buƙatar beli da tsohon gwamnan jihar, Nasiru Ahmed El-Rufai, ya gabatar a gabanta.
A zaman da aka yi a ranar a ranar Litinin, 29 ga Yunin 2026, kotun ta ce El-Rufa'i bai gabatar da isassun hujjoji da za su sa kotu ta yi amfani da ikonta wajen sake shi ba.

Kara karanta wannan
Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu

Source: Twitter
Jaridar Leadershp ta kawo labarin cewa Mai shari'a Justice Diruis Khobo ya bayyana cewa buƙatar belin ba ta da ƙarfi kuma ba ta nuna wasu dalilai na musamman da za su tabbatar da bayar da belin ba.
Tuhumar da ICPC ke yi wa El-Rufa'i
Rahoton Daily Post ya bayyana cewa El-Rufai na fuskantar tuhuma guda tara da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta shigar a kansa, waɗanda suka shafi zargin cin zarafin ofis da wasu laifuffuka masu alaƙa da hakan.
An gudanar da zaman kotun ba tare da El-Rufai ya halarta a zahiri ba lokacin da aka karanta hukuncin kan buƙatar belinsa.
A hukuncinsa, Mai shari'a Khobo ya ce tsohon gwamnan ya kasa gabatar da sahihan hujjoji da takardu masu gamsarwa da za su tabbatar da dacewar a sake shi da beli.
Ya kuma bayyana cewa babu wasu dalilai na musamman da suka fito fili waɗanda za su sa kotun ta amince da belinsa kafin a kammala shari'ar.
Umarnin kotu kan lafiyar El-Rufa'i
Duk da ƙin bayar da belin, kotun ta umarci ICPC ta bai wa El-Rufai cikakkiyar damar ganin tawagar likitocinsa ko kuma zuwa duk wani asibitin da ya zaɓa a cikin Najeriya domin samun kulawar lafiya idan buƙatar hakan ta taso.sssss

Source: Twitter
Haka kuma, Mai shari'a Khobo ya ba da umarnin cewa El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun ICPC har zuwa ci gaba da sauraron shari'ar, sannan ya ɗage zaman zuwa ranakun 7 da 8 ga watan Yuli, 2026.
An fara gurfanar da El-Rufai a gaban Babbar Kotun Kaduna a ranar 18 ga Maris, 2026 tare da Manajan Daraktan kamfanin TMDK Terminal, Amadu Sule, ƙarƙashin lambar shari'a KDH/KAD/ICPC/01/26.
Atiku ya yi magana kan belin El-Rufa'i
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai na ci gaba da zama a tsare bayan ya kasa cika sharuddan belin da aka gindaya masa a shari'ar da gwamnatin Najeriya ke yi da shi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja
Jagoran adawa kuma 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar hamayya ta ADC, Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan tsauraran sharuddan da aka gindaya yayin bayar da belin na Malam Nasir El-Rufai.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa bai kamata beli ya zama wani makami da za a ci gaba yin azabtarwa da shi ba, musamman ganin irin tsauraran sharuddan da aka gindaya masa.
Asali: Legit.ng
