Gemu baya karatu: Wata 'yar shekaru 68 ta koma makarantar firamare

Gemu baya karatu: Wata 'yar shekaru 68 ta koma makarantar firamare

- Wata 'yar shekaru 68 ta koma makarantar firamare

- Tace tsufa ba zai hana ta neman ilimi ba

Lallai maganar Hausawa gaskiya ne da suka ce gemu baya hana ilimi ga dukkan wanda yake da sha'awar hakan domin kuma mun samu labarin wata tsohuwa mai shekaru 68 a duniya da ta koma makarantar Furamare a kasar Kenya.

Gemu baya karatu: Wata 'yar shekaru 68 ta koma makarantar firamare
Gemu baya karatu: Wata 'yar shekaru 68 ta koma makarantar firamare
Asali: UGC

KU KARANTA: Matashi ya kirkiri wani irin injin mai ban mamaki a Najeriya

Matar mai suna Veronicah Kaleso kmar yadda muka samu ta koma makarantar ne sannan kuma ta zana jarabawar kammala furamare tare da sauran 'yan kasar a makarantar Unoa dake a garin Makueni.

Legit.ng Hausa ta samu cewa Veronicah Kaleso ta bar makaranta ne tun a shekarun 1960 amma bata samu ta koma ba sai a wannan lokacin domin ta inganta rayuwar ta da ta sauran al'umma, kamar yadda tace.

Veronicah Kaleso ta kara da cewa ta koma makaranta ne domin ta kara samun ilimin gudanar da sana'ar ta ta noma domin a halin yanzu zamani ya zo da abubuwa da dama da suke bukatar ilimin zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng