A Wata 1 Kacal, Hukumar Kwastam Ta Tara Kudin Shiga Sama da Naira Biliyan 100 a Tashar TinCan
- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta tara Naira biliyan 111.2 a tashar ruwa ta Tin Can Island da ke Legas a watan Mayun 2026
- Sabon shugaban kwastam mai kula da wurin, Joseph Anani, ya ce zai ƙara inganta kuɗaɗen shiga da sauƙaƙa harkokin kasuwanci
- Ya yaba wa jami'ai da masu ruwa da tsaki kan bin doka da ƙa'ida da suka taimaka wajen samun nasara a cikin wata guda kadai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos – Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) da ke Tashar Jiragen Ruwa ta Tin Can Island (TCIP) ta bayyana cewa ta samu kuɗaɗen shiga har Naira biliyan 111.2 a watan Mayun shekarar 2026.
Sabon Kwanturolan yankin, Joseph Anani, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a hedkwatar hukumar da ke Legas.

Kara karanta wannan
An sake samun tangarda a shari'ar da ake zargin Ganduje da karkatar da kuɗaɗen jihar Kano

Source: Facebook
A rahoton The Nation, ya ce kwastam za ta ci gaba da aiki tukuru bayan wannan nasara tare da ƙoƙarin ƙara yawan kuɗaɗen shiga fiye da yadda aka samu a baya.
Abin da ya haifar da nasarar kwastam
Anani ya bayyana cewa samun wannan kuɗi mai yawa ya samo asali ne daga jajircewar jami'an kwastam, bin doka da ƙa'ida da masu ruwa da tsaki suka yi, da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyuka.
Ya ce:
“Ina farin cikin sanar da ku cewa kwastam na samun gagarumar nasara wajen tara kuɗaɗen shiga. Wannan ya samo asali ne daga ƙwazon jami’anmu, bin ƙa’ida da kuma ingantaccen tsarin gudanar da aiki.”
Ya ƙara da cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ci gaba da samun wannan nasara tare da ƙoƙarin zarce abin da aka samu a lokacin shugabancin da ya gabata.
Kwastam ta shirya karfafa bin doka
Kwanturolan ya tabbatar da cewa za su ci gaba da ɗaukar matakan bin doka, haɗa kai da masu gudanar da harkokin tashar jiragen ruwa da kuma amfani da fasahar zamani domin sauƙaƙa kasuwanci na halal da ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Ya jaddada cewa duk ayyukan Kwastam za su ci gaba da tafiya daidai da tanadin Dokar Hukumar Kwastam ta 2023.
A cewarsa, shirye-shiryen zamanantar da hukumar da ake aiwatarwa a yanzu za su taimaka wajen inganta aiki, ƙarfafa bin doka da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

Source: Twitter
Kwastam ta yabawa 'yan jarida
Anani ya bayyana kafafen yaɗa labarai a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a ayyukan hukumar, cewar rahoton Vanguard.
“Tun bayan zuwana nan, na sanya hulɗa da dukkan masu ruwa da tsaki a matsayin babban abin da na sa a gaba, kuma kafafen yaɗa labarai na daga cikin mafi muhimmanci a wannan tsari," in ji shi.
An kara wa shugaban kwastam wa'adi
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , ya ƙara tsawaita wa’adin aikin shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi da watanni shida.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da wa'din shekara guda da Shugaba Bola Tinubu ya kara masa a bara ke dab da karewa.
Tun da farko, wa’adinsa zai ƙare ne a ranar 31 ga Agustan 2025 bayan cika shekaru 35 yana aiki, amma shugaban ƙasa ya ƙara masa shekara guda, wadda ake sa ran za ta ƙare a watan Agustan 2026.
Asali: Legit.ng
