'Ku Kara Hakuri,' Manoma Sun Fadi Lokacin da Tumatir Zai Yi Araha a Najeriya
- Kungiyar masu noman tumatir ta Najeriya ta ce farashin tumatir da ya yi tashin gwauron zabi zai fara sauka daga ƙarshen Yuli
- Shugaban TOPAN, Rabiu Zuntua ya bayyana cewa fara girbin tumatirin damina zai kara yawan kaya a kasuwa tare da rage matsin farashi
- Kungiyar ta bukaci gwamnati da masu zuba jari su samar da wuraren ajiya domin rage asarar amfanin gona da manoma ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - Kungiyar masu noman tumatir da sarrafa shi ta Najeriya (TOPAN) ta bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa hauhawar farashin tumatir da ake fuskanta a yanzu zai ragu sosai daga ƙarshen watan Yuli.
Shugaban TOPAN na jihar Kaduna, Rabiu Zuntu, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Legas.

Source: Getty Images
Me ya jawo tashin farashin tumatir?
Rahoton Vanguard ya nuna cewa farashin tumatir ya yi matukar tashi tun farkon watan Mayu sakamakon karewar girbin damina da kuma raguwar kayan da ake samu a kasuwa.
A yanzu, kwandon tumatir mai nauyin kilo 50 wanda a watan Janairu ake sayar da shi tsakanin N18,000 zuwa N20,000, ya kai tsakanin N100,000 zuwa N130,000 gwargwadon iri.
Haka kuma, kwandon kilo 25 a manyan kasuwannin Legas yanzu yana kaiwa tsakanin N50,000 zuwa N70,000.
Girbin damina zai kawo sauki
Rabiu Zuntu ya ce tashin farashin ba sabon abu ba ne, domin yanayi ne da ake fuskanta a wasu lokutan shekara.
Ya bukaci ‘yan Najeriya su kara hakuri, yana mai cewa farashin zai fara raguwa da zarar manoma sun fara girbin tumatirin damina.
Ya ce:
“Mun yi hasashen cewa karin farashin tumatir zai ci gaba har zuwa ƙarshen Yuli, lokacin da girbin damina zai fara.
“Daga watan Agusta, farashi zai fara sauka sosai saboda sabbin kaya za su shiga kasuwa.”
Sababbin iri sun taimaka wa manoma
Shugaban TOPAN ya ce amfani da sababbin nau’ikan tumatir masu jure ambaliya ya bai wa manoma damar ci gaba da noma a lokacin damina.
A cewarsa, hakan zai kara yawan amfanin gona tare da kawo saukin farashi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce idan manoma ba su rungumi wadannan sabbin nau’ikan ba, da al’umma sun jira har zuwa Oktoba ko Nuwamba kafin farashin ya fara sauka.

Source: Getty Images
Canjin yanayi na kara matsalar noma
Shugaban kungiyar ya danganta karancin tumatir da ake samu tsakanin watan Mayu da Yuni da tasirin sauyin yanayi.
Ya ce sauyin ruwan sama da tsananin zafi sun rage damar noman tumatir a manyan jihohin da ke noma shi kamar Kaduna da Kano.
Ya kara da cewa samar da irin tumatir da ke jure zafi zai taimaka wajen kara yawan noma idan aka samar da shi ga manoma.
NBS: Farashin kayan abinci ya tashi
A wani labari, mun ruwaito cewa, Hukumar kididdiga ta kasa ta ce hauhawar farashin kaya a Najeriya ta tashi daga 15.69% zuwa 15.93% a watan Mayun 2026.
Farashin kayan abinci kamar albasa, masara, tumatir da doya sun taka rawa wajen tashin farashin abinci a fadin kasar nan.
Jihohin Yobe, Anambra da Sokoto ne suka fi fama da hauhawar farashi yayin da Niger da Plateau suka samu saukin hauhawar.
Asali: Legit.ng


