Bayan Mutuwar Jigo a Izala, Tsohon Shugaban APC Ya Rasu a hannun Yan Bindiga

Bayan Mutuwar Jigo a Izala, Tsohon Shugaban APC Ya Rasu a hannun Yan Bindiga

  • Tsohon shugaban APC daga jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa jigon APC ya mutu a daji bayan shafe makonni da dama a hannun maharan
  • Rahotanni sun nuna cewa mutanen biyu da suka bayyana a bidiyon da aka saki daga dajin Birnin Gwari sun mutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi, Kebbi - Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa wani jigon jam'iyyar APC mai mulki ya rasa ransa.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Koko/Besse a Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasu yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga.

Tsohon shugaban APC ya mutu a hannun yan bindiga
Shugaban Izala, Yahaya Billi da tsohon shugaban APC a karamar hukumar Koko/Besse, Muhammadu Mai Barga lokacin da suke hannun yan bindiga kafin mutuwarsu. Hoto: @DanKatsina50.
Source: Twitter

An bayyana mutuwarsa ne ranar Talata 23 ga watan Yunin 2026 ta hanyar wani sako daga shafin Bakatsine wanda ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je gidan shugaban APC sun sace masa iyalai a Kebbi

Yadda aka sace dattawa 2 a Kebbi

Majiyoyi sun ce an yi garkuwa da Besse ne a farkon watan Yunin shekarar 2026, kuma tun daga lokacin iyalansa da magoya bayansa suka kasance cikin damuwa da fargaba.

A baya, wani rahoto ya bayyana wanda ya nuna Besse tare da wani abokinsa, Yahaya Billi yayin da ‘yan bindiga ke muzanta su a cikin dajin Birnin Gwari.

Cikin mutanen da aka kama, wanda shi ne tsohon shugaban APC, dayan kuma ya bayyana cewa shi malamin makaranta ne.

Sun yi kira da a taimaka musu suna cewa ba su da lafiya:

"Idan so ku ke mu mutu, sai ku fada mana mu yi sallama da ku mu mutu. Yanzu ga Yahaya nan ba shi da lafiya. Ni ma kun san ba ni da lafiya, kullum sai na sha magani."

Yan bindiga: Tsohon shugaban APC ya mutu

An tabbatar da cewa Alhaji Muhammadu Mai Barga Besse ya mutu yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano

Wannan na nufin mutanen biyu da suka bayyana a bidiyon da aka fitar daga dajin Birnin Gwari duk sun rasa rayukansu.

Rahoton ya nuna cewa babu daya daga cikinsu da ya samu damar sake haduwa da iyalansa bayan sace su da aka yi.

An bayyana cewa abin da ya fara da wani bidiyo mai tayar da hankali ya kare da mummunar asara ga iyalai biyu, cewar DailyPost.

Mutuwar mutanen biyu ta kara jawo tambayoyi masu yawa kan matsalar tsaro da ke addabar al’ummomi a sassan Arewacin Najeriya.

A karshe, an yi addu’ar Allah Ya gafarta musu kurakuransu, Ya sanya su a Aljannatul Firdausi tare da ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.

Shugaban Izala ya rasu a hannun yan bindiga

A baya, mun ba ku labarin cewa an sanar da rasuwar shugaban Izala na Besse, Malam Yahaya Billi bayan shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane.

An tabbatar da cewa an sace Yahaya Billi ne tare da wani dattijo wanda ya kasance tsohon shugaban APC a karamar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi.

An bukaci al'umma su halarci Sallar Ga'ib da za a gudanar a Garkan Sarki da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a jihar Kebbi da ke fama da hare-haren yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.