INEC Ta Fitar da Alkaluma, Kano Ta Shiga Gaba a Yawan Sababbin Masu Rijistar Zabe a Najeriya
- Hukumar INEC ta bayyana Kano a matsayin jihar da ta fi samun yawan sababbin masu rijistar kada kuri'a a fadin Najeriya
- Alkaluman da INEC ta fitar sun nuna cewa yan Najeriya sama da 500,000 sun yi rijistar kada kuri'a zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2026
- Haka zalika bayanai sun nuna cewa mata su ne a gaba wajen yawan yin rijistar katin zabe yayin da ake ci gaba da aikin a fadin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi rajistar sababbin masu kada kuri’a 581,298 a fadin Najeriya zuwa ranar 29 ga watan Mayu, 2026.
Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa mutum 321,921 ne suka kammala rajista ta yanar gizo, yayin da wasu 259,377 suka kammala rajista a cibiyoyin rajista.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun buga da ƴan bindiga da suka yi yunkurin garkuwa da mutane a Kano

Source: Twitter
Hakan ya sa jimillar sababbin mutanen da suka yi rajistar kada kuri’a ya kai 581,298, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta rahoto.
Kano ta shiga gaba a yawan masu rajista
Bayanan INEC sun nuna cewa jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan sababbin masu rajista da mutum 49,603 yayin da jihar Sokoto ta zo ta biyu da mutum 32,293, sai kuma Lagos ta kasance ta uku da mutum 27,294.
Sauran jihohin da suka samu yawan rajista sun hada da Jigawa – 26,576, Kaduna – 26,449, Taraba – 24,516, Niger – 24,278, Nasarawa – 22,829, Gombe – 21,813 da Katsina – 21,525
A daya bangaren kuma, Abuja ta samu mutum 8,350 da suka yi rajista, yayin da Akwa Ibom ta samu mafi karancin rajista a cikin jihohin da ake gudanar da aikin, da mutum 4,834.
Dalilin dakatar da rajista a Ekiti da Osun

Kara karanta wannan
INEC ta gano yadda aka haɗa baki da jami'inta wajen ba hadimin Wike bayanan katin zabe
INEC ta bayyana cewa har yanzu an dakatar da rajistar masu kada kuri’a a jihohin Ekiti da Osun saboda shirye-shiryen zabukan gwamna da ke tafe a jihohin biyu, wanda hakan ya yi daidai da tanadin dokar zabe ta 2022.
Ta kuma jaddada cewa alkaluman da aka fitar na wucin gadi ne, domin har yanzu za a gudanar da tantance bayanai da cire rajistar da aka yi fiye da sau daya.

Source: Twitter
Mata sun fi maza yin rajistar zabe
Bayanan INEC sun nuna cewa mata ne suka fi yawa a cikin sababbin masu rajistar kuri'a, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Daga cikin mutum 581,298 da suka kammala rajista, akwai mata 304,256 (52.34% da maza: 277,042 (47.66%).Wannan na nuna cewa mata sun fi maza shiga cikin aikin rajistar masu kada kuri’a a wannan zagaye.
INEC ta gargadi jam'iyyun siyasa
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta gargadi jam’iyyun siyasa game da zaɓen fitar da gwani a Najeriya.
INEC ta ce duk wani zaɓen fitar da gwani da aka gudanar bayan wa’adin ranar 30 ga Mayu 2026 da ta gindaya ba za ta amince da shi ba.
Hakazalika hukumar ta umarci jam’iyyun siyasa su bi sauran jadawalin ayyukan zaɓe da ta fitar domin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng