Tinubu Ya Zakulo Matashi Ɗan Shekara 40 Ya Naɗa Shi Sabon Shugaban Hukumar JAMB
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar JAMB bayan karewar wa’adin Is-haq Oloyede
- Farfesa Segun Aina zai karbi ragamar hukumar daga ranar 1 ga watan Agustan 2026 bayan kammala wa’adin shekaru biyu na Farfesa Oloyede
- Gwamnati ta bayyana sabon shugaban JAMB a matsayin gogaggen masani a fannin tsarin jarabawa, fasahar zamani da gyaran hukumomin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta JAMB.
Farfesa Aina, wanda zai cika shekaru 40 a watan Yuli, zai maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede wanda wa’adinsa na biyu zai kare a ranar 31 ga watan Yulin 2026.

Source: Twitter
Tinubu ya nada sabon shugaban JAMB
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, a shafinsa na X.
Fadar shugaban kasa ta yabawa sabon shugaban JAMB tare da bayyana gogewarsa a harkokin ilimi da fasahar zamani
A cewar Onanuga, Farfesa Segun Aina gogaggen malami ne kuma masani a fannin tsarin kwamfuta da gyaran cibiyoyin gwamnati.
Sanarwar ta ce:
“Yana da digirin farko a fannin injiniyancin Computer Systems daga jami’ar Kent da ke Birtaniya.
“Haka kuma yana da digirin digirgir da na biyu a fannin Internet Computing and Network Security da kuma Digital Signal Processing daga jami’ar Loughborough.”
Burin Tinubu kan sabon shugaban JAMB
An kuma bayyana cewa Farfesa Aina ya halarci shirin horar da manyan jami’ai a babbar makarantar kasuwanci ta Legas (LBS).
Tinubu ya bukaci sabon shugaban JAMB ya kara bunkasa nasarorin da Oloyede ya samu a hukumar, a cewar rahoton Daily Trust.
Fadar shugaban kasa ta ce sabon shugaban JAMB ya taba aiki da hukumar a lokacin bautar kasarsa ta NYSC, inda ya samu kwarewa a harkokin tsarin daukar dalibai da sarrafa bayanai.
Bayo Onanuga ya ce shugaban kasa na fatan Farfesa Aina zai yi amfani da kwarewarsa wajen kara inganta ayyukan JAMB tare da dorawa daga inda Farfesa Oloyede ya tsaya.

Source: UGC
Aina ya zama farfesa da kuruciya
An bayyana cewa yana cikin kungiyoyin kwararru da suka hada da COREN, NSE, IEEE da kuma IET.
Wani rahoto na Business Day ya nuna cewa Aina ya zama farfesa a fannin injiniyancin na'ura mai kwakwalwa yana da shekaru 39, wanda ya sa ya zama matashi na farko da ya kai matsayin a wannan fanni.
A lokacin da ya samu wannan matsayi, Aina ya ce:
"Wannan gagarumar nasara babban darasi ne dake tunatar da mu cewa ƙwazo, tarbiyya, da kuma gudanar da aiki cikin manufa za su iya hanzarta samar da ci gaba.
"Ina kallon wannan matsayi na farfesa ba a matsayin matakin ƙarshe ba, a'a, wani sabon nauyi ne da aka ɗora mini don ba da gudummawa mafi ma'ana ga fannin ilimi, masana'antu, da kuma ci gaban ƙasa."
Mafi karancin makin shiga jami'a daga JAMB
A wani labari, mun ruwaito cewa, JAMB ta kayyade maki 150 a matsayin mafi karanci ga wadanda ke neman gurbin shiga jami'o'i a shekerar 2026 a Najeriya.
An cimma wannan matsaya ne a taron tsara manufofin ba da guraben shiga manyan maiaratu, wanda ya gudana a Abuja yau Litinin.
Taron ya samu halartar Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, tare da shugabannin jami’o’i, kwalejojin fasaha da na ilimi da sauran masu ruwa da tsaki.
Asali: Legit.ng


