'Idanuwan El Rufa'i Sun Kumbura,' An Ce ICPC Ta Hana Shi Ganin Likita

'Idanuwan El Rufa'i Sun Kumbura,' An Ce ICPC Ta Hana Shi Ganin Likita

  • Hadimin Nasir El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya zargi hukumar ICPC da hana tsohon gwamnan samun kulawar likita duk da ciwon ido da ke fama da shi
  • A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Adekeye ya ce Nasir El-Rufai ya koka cewa idanunsa sun kumbura, sun yi ja kuma suna masa kaikayi
  • Ya ce ‘yan uwa da suka kai masa ziyara sun sanar da jami’an ICPC halin da yake ciki tare da neman a ba shi kulawar likita amma bai samu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hadimin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya zargi ICPC da gaza ba tsohon gwamnan kulawar likita duk da korafinsa kan matsalar idanunsa da ke ƙara tsananta yayin da yake tsare.

Kara karanta wannan

"Asiri zai tonu," Ana zargin ba tsakani da Allah Kwankwaso ya hada kai da Peter Obi ba

An tsare El-Rufa'i ne bisa zarge-zarge da aka gabatar masa tun bayan dawowar shi daga kasar Masar a kwanakin baya, kuma ya shafe sallar azumi da layya a tsare.

Nasir El-Rufa'i kafin ICPC ta kama shi
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Facebook

Idon El-Rufa'i ya kumbura

A cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda the Cable ta ruwaito, Muyiwa Adekeye ya yi zargin cewa idanun El-Rufai sun kumbura, sun yi ja kuma suna masa kaikayi ba tare da an kawo masa likita ba.

A cewar Adekeye, ‘yan uwa da suka kai wa tsohon gwamnan ziyara sun lura da halin da yake ciki kuma sun roƙi jami’an ICPC su taimaka wajen samar masa da kulawar likita.

Hadimin ya ce jami’ai biyu na hukumar ICPC sun duba idanun El-Rufai amma ba a samar masa da wata ƙarin kulawar likita ba.

Hadimin El-Rufa'i ya karyata ICPC

Adekeye ya kuma yi zargin cewa wani jami’in ICPC mai suna Henry ya gaya wa wani ɗan uwan El-Rufai cewa tsohon gwamnan ba ya son ganin likita, zargin da ya bayyana a matsayin ƙarya da rashin tausayi.

A cewarsa, tun da farko an kai El-Rufai wani asibitin ido a ranar 4 ga Yunin 2026, amma an ce halin da yake ciki ya ƙara muni cikin dare.

Kara karanta wannan

Farashin danyen mai ya ruguzo bayan Trump ya hana Isra'ila kai hari Lebanon

Vanguard ta rahoto Adekeye.ya ce:

“Matansa da suka kai masa ziyara a yau sun same shi cikin tsananin rashin jin daɗi kuma sun firgita da yadda idanunsa suke,”

Ya kuma bayyana cewa lauyoyin El-Rufai sun riga sun samu umarnin kotu da ya ba shi damar ganin likitocinsa da samun kulawar likita saboda matsalolin lafiyar idanunsa da ke yawan tasowa yayin da yake tsare.

Nasir El-Rufa'i da jami'an tsaro
Lokacin da aka kai Nasir El-Rufa'i kotu a Kaduna. Hoto: Uche Diala
Source: Facebook

Adekeye ya zargi hukumar da yin watsi da umarnin kotu da kuma nauyin da ke kanta na kula da mutumin da ke hannunta.

Bello El-Rufai ya samu tikitin ADC

A wani labarin, kun ji cewa Bello El-Rufai ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ADC na kujerar mazabar tarayya ta Kaduna ta Arewa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Bello, ɗan Nasir El-Rufai, ya ce ya samu ƙuri’u 7,727 a zaɓen fitar gwani na ADC na kujerar mazabar tarayyar.

Ɗan majalisar tarayyar ya yaba wa masu ruwa da tsaki da mambobin ADC saboda gagarumin nuna amincewa da yarda da suka yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng