Sarki Sanusi II Ya Yi Magana kan Beli 'Mai Tsauri' da aka Saka wa El Rufa'i

Sarki Sanusi II Ya Yi Magana kan Beli 'Mai Tsauri' da aka Saka wa El Rufa'i

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai inda ya ce yana fuskantar tsauraran sharuɗan beli
  • Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi zargin cewa an buƙaci sarki da babban jami’in gwamnati su tsaya wa El-Rufa'i a matsayin masu lamunin belinsa
  • Bayan batun Nasir El-Rufa'i, Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda tarbiyya ta yi kadan a Arewacin Najeriya da raguwar tasirin siyasar yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na fuskantar tsauraran sharuɗan beli kafin a sake shi daga tsarewar hukumar ICPC.

El-Rufai yana hannun ICPC tun daga ranar 19 ga Fabrairun 2026 bisa zargin almundahanar kuɗi a lokacin mulkinsa na gwamnan Kaduna tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi, shugabannin Kirista sun yi kira da murya daya kan matsalar tsaro

Nasir El-Rufa'i da Sarki Sanusi II
Nasir El-Rufa'i a hagu da Sarki Muhammadu Sanusi II a dama. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Masarautar Kano
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa A ranar 13 ga Afrilun 2026, ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan a babbar kotun jihar Kaduna kan sabunta tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin zamba da kuma amfani da mukami ba daidai ba.

Korafin Sanusi kan belin El-Rufa'i

Da yake magana da manema labarai bayan wani taro, Sanusi II ya yi zargin cewa hukumomi sun buƙaci wani sarki da kuma babban jami’in gwamnati su tsaya wa El-Rufai a matsayin masu lamuni kafin a sake shi.

“Misali, ku dubi abin da ke faruwa da ɗan’uwana, Malam Nasir el-Rufai. A yanzu yana tsare, kuma sharuɗan da aka gindaya domin a sake shi suna da matuƙar wahala,”

In ji Sarki Sanusi

“Sun ce dole ne wani sarki da kuma babban ma’aikacin gwamnati su sanya hannu a belinsa.”

Korafi kan matsalolin Arewa

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da ya koma sarki ya kuma yi alhinin raguwar tarbiyya wajen mu'amala da raya al’adun Arewacin kasar.

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

Sanusi II ya ce talauci ya daɗe yana addabar yankin, amma a tarihi al’ummar Arewa sun kasance masu mutunta kansu tare da mayar da al’amuransu ga Allah duk da matsin tattalin arziƙi.

Sarki Muhammadu Sanusi II
Sarki Sanusi II yayin zaman fada a Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Twitter
“Dangane da Arewa, dukkanmu mun san cewa talauci ya daɗe yana addabar yankin nan. Duk da haka, duk da talaucinsu, mutanen Arewa suna mutunta kansu tare da barin komai a hannun Allah maɗaukakin sarki,”

In ji shi.

“Abin da ke damun Arewa ba kawai rashin kuɗi ba ne, illa rushewar al’adunmu da kuma yunƙurin kwaikwayon wasu al’adu.”

Tahir Prime ya wallafa bidiyon da Sanusi II ya yi bayani a X:

Sanusi ya yi wa Shettima raddi

A wani labarin, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi ya yi wa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima raddi kan wasu kalamai da ya yi.

A wani taron tattalin arziki a Legas, Kashim Shettima ya bayyana cewa jihar ce ta samar da Aliko Dangote da Abdul Samad Rabiu ba Kano ba.

Sai dai Sarki Sanusi II ya masa martani da cewa manyan masu kudin Najeriya da Afrika sun kafa tubalin arzikinsu ne a Kano ba Legas ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng