Manoma fiye da 128,500 daga Jihohi 25 Za Su Samu Tallafin Buhunan Taki a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya za ta raba buhunan taki 515,720 ga manoma 128,930 a jihohi 25 da Abuja don bunƙasa noma da samar da abinci
- Shirin FISP na NADF ya mayar da hankali kan ƙananan manoma masu noma ƙasa da rabin hekta domin rage kuɗin noma da wadatar abinci
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya fadi fa'idojin shirin ga Najeriya yayin da ya bada tabbaci kan gaskiya wajen rabon takin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da rabon buhunan taki 515,720 na urea da NPK ga manoma 128,930 a jihohi 25 da birnin tarayya Abuja.
Wannan yana daga cikin wani yunƙuri na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙarfafa harkar noma da bunƙasa samar da abinci a ƙasar nan.

Source: Twitter
Shettima ya ƙaddamar da shirin rabon taki
Shettima ya ƙaddamar da shirin ne a Abuja a ƙarƙashin shirin tallafin kayan noma na Renewed Hope - FISP, wanda Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa (NADF) ke gudanarwa, inji rahoton Daily Trust.
Da yake jawabi ta bakin ministan noma da tsaron abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, Shettima ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙara yawan amfanin gona, tabbatar da wadatar abinci da inganta rayuwar manoma.
Ya ce wannan tallafi ya yi daidai da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na farfaɗo da tattalin arziki da samar da ci gaba ga al’umma.
A cewarsa, rabon takin ya nuna ƙudirin gwamnati na tallafa wa manoma da ƙara ƙarfin samar da abinci a Najeriya.
Manoma a Abuja za su amfana
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa za a raba buhunan taki 11,210 ga manoma 2,930 da suka yi rajista a Babban Birnin Tarayya.
Ya ƙara da cewa shirin ya fi karkata ne ga ƙananan manoma masu noma ƙasa da rabin hekta, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a faɗin ƙasar.
Shettima ya kuma buƙaci masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa takin ya kai ga waɗanda aka tanada masa, musamman mata, matasa da sauran manoma masu buƙata.

Source: Twitter
An jaddada muhimmancin wadatar abinci
Babban Sakataren NADF kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Mohammed A. Ibrahim, ya ce an fara aiwatar da shirin ne a daidai lokacin da manoma ke buƙatar kayan noma domin rage kuɗaɗen samarwa da kuma ƙara yawan amfanin gona.
Ya bayyana cewa wadatar abinci na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiyar tattalin arziki, bunƙasa karkara da samar da ayyukan yi, in ji rahoton The Nation.
Ibrahim ya ce duk takin da ake rabawa a ƙarƙashin shirin an samar da shi ne a cikin gida, kuma an yi masa alamar “Ba na Siyarwa Bane” domin hana karkatar da shi zuwa kasuwa.
Gwamna zai rabawa manoma taki
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya ce manoma a jihar za su sayi takin zamani a kan farashin tallafi na N28,000 a kowane buhu.
Gwamna Alia ya bayyana cewa za a sayi takin ne kan farashi mai rahusa a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin haɓaka ayyukan noma.
Ya jaddada sadaukarwar gwamnatinsa wajen haɓaka fannin noma na zamani kuma mai amfani ga kasuwanci, wanda ke da ikon samar da ayyukan yi, rage fatara, da kuma samar da ci gaban tattalin arziki.
Asali: Legit.ng


