Za a Kashe N83bn kan Ambaliya a Najeriya, Shettima Ya Yi Muhimmin Kira ga Jihohi
- Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta amince da kashe Naira biliyan 83.2 domin dakile ambaliyar ruwa da sauran bala’o’in da ake sa ran za su afku
- Mataimakin shugaban kasa ya bukaci jihohi su hada kai da gwamnatin tarayya wajen warware matsalolin fitar da kayan noma kasuwannin duniya
- Kashim Shettima ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta daina fitar da kayayyakin noma da ba a sarrafa ba zuwa waje, wanda a karshe ake dawo da su kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) ta amince da ware Naira biliyan 83.2 domin aiwatar da shirye-shiryen rigakafin ambaliyar ruwa da sauran bala’o’in da ake sa ran za su afku a sassan Najeriya.
An amince da kudin ne a taro na 158 na majalisar da aka gudanar ranar Alhamis karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta fitar da Naira miliyan 50, za a tallafawa masu fama da cutar daji

Source: Twitter
Dalilin amincewa da kashe N83.2bn
Sanarwar da aka wallafa a shafin fadar shugaban kasa, ta nuna cewa amincewar ta biyo bayan gabatarwar da Karamin Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya yi kan bukatar daukar matakan kariya tun kafin aukuwar ambaliya, musamman a wannan lokaci na damina.
Majalisar ta bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta daina jiran bala’o’i su afku kafin daukar mataki, tana mai jaddada muhimmancin shirin AATF wajen dakile illolin da ka iya tasowa.
Shettima ya bukaci sakamako a aikace
Da yake jawabi a wajen taron, Kashim Shettima ya ce dole ne sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa su fara samar da sakamako a rayuwar talakawan Najeriya.
Ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati da irin tasirin da manufofinta ke yi ga manoma, masana’antun cikin gida, matasa marasa aikin yi da sauran masu bukatar tallafi.
“Ba a auna nasarar tsare-tsare da abubuwan da aka rubuta a takardu ba, ana auna su ne da sakamakon da suke haifarwa a rayuwar jama'a,” in ji Shettima.

Source: Twitter
Kira kan fitar da kayan noma
Mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi su hada kai da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da ke hana kayan noma na Najeriya isa kasuwannin duniya.
Ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ba zai bunkasa yadda ya kamata ba muddin kasar na ci gaba da fitar da albarkatun kasa ba tare da sarrafa su ba, in ji rahoton Punch.
Shettima ya ce akwai bukatar gina cikakken tsarin samar da kayayyaki daga gona zuwa masana’antu, daga masana’antu zuwa tashoshin jiragen ruwa, sannan zuwa kasuwannin duniya.
Ya kara da cewa gwamnati za ta mayar da hankali wajen magance matsalolin tashoshin jiragen ruwa da kuma cika ka’idojin da kasuwannin duniya ke bukata domin kara wa manoma da masana’antun Najeriya damar samun riba.
Jihohi 33 za su fuskanci ambaliya
A wani labari, mun ruwaito cewa, ministan albarkatun ruwa, Farfesa Joseph Utsev, ya sanar da cewa garuruwa 14,118 a ƙananan hukumomi 266 za su fuskanci barazanar ambaliya.
Jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne aka yi hasashen cewa ambaliyar za ta shafa tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2026.
Manyan birane kamar Legas, Kano, Abuja, da Kaduna za su fuskanci ambaliya mai tsanani sakamakon toshewar magudanun ruwa a jihohinsu.
Asali: Legit.ng

