'Aure Bautar Maza ne,' Jaruma Nafisat Abdullahi ba ta Shirya zuwa Dakin Miji ba

'Aure Bautar Maza ne,' Jaruma Nafisat Abdullahi ba ta Shirya zuwa Dakin Miji ba

  • Jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi ta jawo ce-ce-ku-ce bayan bayyana cewa aure ba ya gabanta, tana mai cewa ba ta son zama a ƙarƙashin namiji
  • Nafisah Abdullahi ta nuna kin amincewa da ra'ayin cewa haihuwa na tabbatar da samun kulawa idan mutum ya tsufa a karshen rayuwar shi ta duniya
  • Kalaman jarumar sun haifar da ra'ayoyi mabambanta tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka soke ta, wasu kuma suka yaba mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jarumar fim din Kannywood, Nafisat Abdullahi ta haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan bayyana ra'ayoyinta kan aure da suka raba kan masu amfani da kafafen.

Jarumar ta fuskanci suka bayan wani bidiyo ya bayyana inda ta yi korafi kan muhimmancin da mata da dama ke bai wa aure.

Kara karanta wannan

N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi

'Yar wasan fim, Nafisah Abdullahi
Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisah Abdullahi. Hoto: Nafisat Abdullahi
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa Nafisat ta ce ba ta fahimci dalilin da zai sa mace ta kwashe shekaru tana gina sana'arta da samun 'yancin cin gashin kanta, sannan daga baya ta miƙa kanta ƙarƙashin ikon wani bayan ta yi aure ba.

Nafisat Abdullahi ba ta shirya aure ba

A bayanin da ta yi, Nafisa Abdullahi ta ce aure ba wani abu ba ne da take buri a rayuwarta domin ba za ta iya tunanin kasancewa ƙarƙashin ikon namiji ba.

“Mace tana wahala, tana gina rayuwarta da dukiyarta, sannan ta shiga ƙarƙashin ikon wani saboda aure. Ban ga dalilin hakan ba,”

In ji ta.

Nafisah ta kuma ƙalubalanci ra'ayin cewa aure da haihuwa na tabbatar da samun kulawa ko addu'o'i a lokacin tsufa ko bayan mutuwa.

Ta ce samun yara ba tabbaci ba ne cewa za su kula da iyayensu ko kuma su ci gaba da yi musu addu'a bayan rasuwarsu, tana mai ƙarawa da cewa tana da 'yan uwa da ke sonta kuma za su ci gaba da tuna ta ko bayan ta mutu.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin Tinubu za ta rusa NBAIS da Sardauna ya kafa wa Musulmai?

Ta ce:

"Da yawan maza gani suke idan sun yi aure sun samu 'yar aiki, kawai kin zama baiwa. A kan me zan tsaya ina damun kai na in je in zama baiwa a gidan wani."
Jaruma Nafisah Abdullah
Jarumar fim a Kannywood, Nafisa Abdullahi. Hoto: Nafisat Abdullahi
Source: Facebook

Jaruma Nafisat Abdullahi ta kuma bayyana cewa da yawa daga cikin masu aure wahala suke sha babu wani dadi a gidan miji.

Maganar auren mai mata

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook, Nafisa Abdullahi ta ce ko da za ta yi aure ba za ta taba auren wanda ya ke da mata ba.

Mutane da dama sun soki jarumar, suna zarginta da yaɗa tunanin da ka iya sa 'yan mata su guji rungumar aure da ake bukata su yi.

Legit ta tattauna da malami

Legit ta tattauna da Malam Muhammad Abubakar da ke koyar da addinin Musulunci a jihar Taraba domin samun karin bayani ko gargadi game da matsayar jarumar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi

Ya ce:

"A Musulunci bai halasta mutum ya ware wani aiki ya ce ba zai aikata ba ba tare da wani dalili ba, musamman wanda aka kwadaitar da yinsa."
"Aure ba bauta wani mutum ba ne. Mace da na miji duk suna daukar dawainiyoyi, saboda cude-ni-in-cu-de-ka ake yi."
"Babu inda aka ce mace ta sauya suna bayan ta yi aure, wasu abubuwan da ake rigima a kansu ba addini ba ne, al'adu ne."

Ana shirin auren gata a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na daf da kammala shirye-shiryen auren gata na shekarar 2026 a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta ware makudan kudi har Naira biliyan 1.5 domin yin hidimar da suka shafi daurawa mutane auren.

Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da cewa za su kawo tsarin da zai hana auren lalacewa, ciki har da hana saki ba tare da sanin Hisbah ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng