“Ai Bana Tunanin Za’a Iya Samun Irinta a Kyau”: Sabbin Hotunan Nafisa Abdullahi Sun Tashi Kan Jama’a

“Ai Bana Tunanin Za’a Iya Samun Irinta a Kyau”: Sabbin Hotunan Nafisa Abdullahi Sun Tashi Kan Jama’a

  • Wasu sabbin hotunan fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi sun bayyana a dandalin soshiyal midiya
  • Hotunan jarumar sun dauki hankalin jama'a da dama, inda suka jinjina kyawunta a matsayinta na bakar mace wacce bata shafe-shafe
  • A ranar Talata ne manyan jaruman masana'antar shirya fina-finan suka halarci liyafar taya shugaban hukumar fina-finai ta kasa, Ali Nuhu murnar samun mukami

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar sabbin hotunan fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi a dandalin soshiyal midiya.

Nafisa na cikin jerin manyan jaruman masana'antar shirya fina-finai da suka halarci bikin taya Ali Nuhu murnar samun mukami a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame malamin addini da matarsa saboda babban laifi 1 da suka aikata

Jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi
“Ai Bana Tunanin Aa’a Iya Samun Irinta a Kyau”: Sabbin Hotunan Nafisa Abdullahi Sun Tashi Kan Jama’a Hoto: @anasko_sheka
Asali: Twitter

Wani mai amfani da shafin X mai suna @anasko__sheka ya wallafa hotunan jarumar tare da jinjina tsantsar kyanta a matsayinta na bakar mace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin ya jaddada cewar lallai Nafisa tana da kyau kuma cewa ya yarda akwai bakaken mata masu kyau.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Karo na farko da na yarda da akwai Black Beauty.
"Maganar gaskiya Nafisa tana da kyau☺️."

Nan take sai mabiya shafin suka tofa albarkacin bakunansu inda mafi akasarin mutane suka goyi bayan hakan, tare da cewar hakan ya kasance ne saboda jarumar bata yi wa fatarta shafe-shafen man bilicin ba.

Martanin jama'a kan hotunan Nafisa Abdullahi

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

@amseer_AMS ya yi martani:

"Kaf kannywood babu me kyau kamarta anuty nafisat Abdullahi "

@luckyOfficial_1:

"Ai bana tunanin za’a iya samun irinta ah kyau. Sabida wannan jikin ba’a yimasa bleaching."

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin yadda 'yan Kannywood suka yi bikin nadin Ali Nuhu mukami a gwamnatin Tinubu

@anasko__sheka ya yi martani"

"Malam je ka sha Bobo kayi bacci ."

@MujaheedKa60532 ya ce:

"Wae nafisah dinnan biyah koh takiyi don kuce tanadah kyau koh."

@eluxeey ya ce:

"Sosai Fa Baba ."

@Usidonguy"

"To amma wannan ai ta tsofa‍♀️ na gani."

@el_yaqub1:

"Inna ganta zuciya na wani bugawa take dawuri wuri ko meyake nufi oho."

@BUSADEEQ"

"Ita kagani Amma bakar mace duniya ce."

@KabiruMusa80873:

"Wannan hakayake fadi ka kara fada."

'Yan Kannywood sun taya Ali Nuhu murna

A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto cewa manyan jaruman Kannywood sun halarci liyafar taya babban jarumi Ali Nuhu murnar samun mukami a gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu.

Ali Nuhu dai shine sabon shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel