An Kama Daruruwan 'Yan Daban da Suka Hana Kano Zaman Lafiya

An Kama Daruruwan 'Yan Daban da Suka Hana Kano Zaman Lafiya

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 345 da ake zargi da aikata laifuffuka tare da kwato makamai masu haɗari 270
  • Dakarun rundunar sun yi haka ne a wani samame na tsaro da aka gudanar na tsawon kwanaki uku a dukkan ƙananan hukumomin jihar
  • Kwamishinan ‘yan sanda, CP Ibrahim Bakori, ne ya bayyana hakan jiya a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a Bompai, Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama aƙalla mutane 345 da ake zargi da daba, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai masu haɗari 270 a faɗin jihar.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan daba ke cigaba da tare hanyoyi a Kano da sace-sacen kayayyaki a kasuwanni da sauransu a fadin Kano.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

Daruruwan 'yan daba a Kano
'Yan daban da aka kama a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Bayanin kwamishinan 'yan sanda

A sakon da kakakin 'yan sanda, Abdullahi Haurna Kiyawa ya wallafa a Facebook, kwamishinan ‘yan sandan Kano, Ibrahim Bakori, ya yi bayani yayin wani taron manema labarai kan halin tsaro a jihar a ranar Litinin.

CP Bakori ya ce wani samame na musamman da aka gudanar na tsawon kwanaki uku a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.

A cewarsa, an gudanar da samamen ne domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka, ƙwace makamai da kuma katse hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.

“Na kira wannan taron ne domin sanar da al’ummar Jihar Kano halin da tsaro yake ciki a yanzu, gabatar da sakamakon samamen da muka gudanar a faɗin jihar, da kuma sake jaddada aniyarmu ta ci gaba da bunƙasa nasarorin da muke samu.
“A yayin samamen, an kama jimillar mutane 345, ciki har da waɗanda ake zargi da daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mutanen da aka samu da makamai masu haɗari.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun baza koma bayan an kama ɗan sandan ƙasar waje da bindiga a Katsina

Ana ci gaba da bincike a kansu kuma za a gurfanar da su a gaban kotu idan hujjoji sun tabbatar da hakan,”

In ji Bakori.

Makaman da aka kama a Kano
Wasu daga cikin kayayyaki da makaman da aka kama a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Makaman da aka kama a Kano

Ya bayyana cewa an kwato makamai masu haɗari 270, ciki har da wuƙaƙe, adda, kulake da sauran kayan aikin da ake amfani da su wajen aikata tashin hankali daga hannun waɗanda ake zargin.

Hakazalika, ya ce an kuma kwato miyagun ƙwayoyi masu yawa da ake zargi haramtattu ne, ciki har da tabar wiwi, ƙwayoyin Exol da sauransu.

CP Bakori ya ce samamen ya rage ƙarfin ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka wajen cutar da jama’a masu bin doka da kuma tayar da zaune tsaye a cikin al’ummomi.

Daba: Gargadin Sheikh Rijiyar Lemo

A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi kira ga gwamnatin Kano kan karuwar 'yan daba.

Malamin ya bayyana cewa 'yan daba sun kara karfi a jihar, inda suke iya toshe hanyoyi domin sata da sauran barna ga al'ummar Kano.

Sheikh Rijiyar Lemo ya bayyana cewa wajibi ne gwamnati ta tashi tsaye wajen kawo karshen su domin hana su kawo ci baya ga jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng