"Dalilan da Za Su Sanya 'Yan Najeriya Su Sake Zabar Bola Tinubu a 2027"

"Dalilan da Za Su Sanya 'Yan Najeriya Su Sake Zabar Bola Tinubu a 2027"

  • Wani jigo a jam'iyyar APC ya bayyana cewa nasarorin Bola Tinubu a fannonin tattalin arziki da ci gaba za su taimaka masa lashe zaɓen 2027
  • Alhaji Abdullahi Ayinde Enilolobo ya ce APC na ci gaba da ƙarfafa tasirinta a ƙasa, inda gwamnoni 32 daga jihohi 36 ke ƙarƙashinta
  • Ya ce yanzu an magance kusan dukkan matsalolin da suka jawo APC ba ta ci zabe a Lagos a 2023 ba, yayin da matasa ke ƙara fahimtar siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lagos – Wani jigon jam’iyyar APC a mazabar Alimosho, Alhaji Abdullahi Ayinde Enilolobo, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Enilolobo ya danganta wannan hasashe da sauye-sauyen tattalin arziki, ayyukan raya ƙasa da kuma ƙarin kuɗaɗen da jihohi ke samu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Yadda Amaechi yake fuskantar matsin lamba kan zama abokin takarar Atiku a ADC

Jigon APC a Lagos ya ce Tinubu zai samu nasara a zaben 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na jawabi a wani taro. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jigon APC ya yi hasashen nasarar Tinubu

Da yake zantawa da manema labarai a Lagos, Enilolobo ya ce matakan da Tinubu ke ɗauka wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da magance matsalolin tattalin arziki za su sa ya samu goyon bayan masu zaɓe a faɗin Najeriya, in ji rahoton The Nation.

Ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya nuna jajircewa wajen gudanar da shugabanci tun bayan hawansa karagar mulki a 2023.

Jigon na APC ya kuma yi nuni da yadda jam’iyyar ke ci gaba da faɗaɗa tasirinta a siyasar Najeriya, yana mai cewa gwamnoni 32 cikin jihohi 36 na ƙasar suna ƙarƙashin APC.

A cewarsa, wannan alama ce da ke nuna yadda jama'a ke ƙara amincewa da shugabancin Tinubu da kuma manufofin jam’iyyar.

Dalilan da ya ce za su taimaka wa Tinubu

Ya kuma ce mambobin APC a Alimosho da sauran sassan jihar Lagos sun fi haɗin kai da shiri a yanzu idan aka kwatanta da lokacin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Rai ya baci: Gwamna zai kori hadiman shi da suka ki shiga APC cikin sa'o'i 48

Enilolobo ya yi ikirarin cewa abubuwan da suka yi tasiri ga sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a wasu yankunan Lagos a shekarar 2023 sun canza sosai.

Ya danganta sakamakon wancan lokaci da ra'ayoyin ƙabilanci da kuma tasirin gwagwarmayar matasa da ta biyo bayan zanga-zangar EndSARS.

A cewarsa, yanayin siyasar yanzu ya bambanta, yayin da matasa da dama suka fi fahimtar al'amuran siyasa kuma tasirin wasu ra'ayoyi ya ragu.

Jigon APC a Legas, Alhaji Abdullahi Ayinde Enilolobo ya hango nasarar Tinubu a zaben 2027.
Alhaji Abdullahi Ayinde Enilolobo, jigon APC da ya ce Tinubu zai lashe zaben 2027. Hoto: Kayode Olayinka
Source: Facebook

Nasarar sauye sauyen tattalin arziki

Ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta gaji ƙasar cikin mawuyacin hali na tattalin arziki, amma ta ɗauki matakan da suka fara haifar da sakamako mai kyau.

Enilolobo ya ce jihohi yanzu suna samun ƙarin kuɗaɗen shiga domin gudanar da ayyukan ci gaba, yayin da matsalolin bashin albashi suka ragu a wasu wurare.

Haka kuma ya yi nuni da raguwar farashin wasu kayayyakin abinci, musamman shinkafa, da kuma alamun daidaituwar darajar naira.

'Tinubu zai samu nasara a Arewa'

A wani labari, mun ruwaito cewa, Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce ayyukan ci gaba da gwamnatin Bola Tinubu ke aiwatarwa a Arewa za su tabbatar masa da nasara a 2027.

Kara karanta wannan

NNPP ta zargi Kwankwaso da yi mata kamun kazar kuku, ta mika bukata ga INEC

Jigon APC ya lissafo manyan ayyukan Tinubu da suka hada da tituna, layin dogo, bututun iskar gas da noma da ke gudana a jihohin Arewa.

Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce dimbin ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke yi sun kara karfafa goyon bayan al’umma ga Shugaba Tinubu a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com