Zaben Fitar da Gwani: APC Ta Yi Martani bayan Tsohon Sufeta Janar Ya Fice daga Cikinta

Zaben Fitar da Gwani: APC Ta Yi Martani bayan Tsohon Sufeta Janar Ya Fice daga Cikinta

  • Jam’iyyar APC a Nasarawa ta yi martani bayan ficewar tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu
  • Shugaban APC na jihar, Aliyu Bello, ya buƙaci magoya bayan Adamu su amince da sakamakon zaɓen fitar da gwani, yana mai cewa iko daga Allah yake
  • Bello ya ce kona tsintsinya ba zai lalata tasirin APC ba, yana mai yabawa ayyukan gwamnati da ci gaban da aka samu a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi magana bayan rasa babban jigonta da ya bar cikinta.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon Sufeto Janar na yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani na gwamna da aka yi.

Tsohon sufeta janar ya bar APC
Mohammed Adamu Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Wali Vanguard.
Source: Facebook

Da yake jawabi, shugaban APC a Nasarawa, Aliyu Bello ya roƙi magoya bayan tsohon Sufeto Janar su karɓi sakamakon zaɓen da hannu bibbiyu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

2027: Salon Peter Obi ya fita daban, ya bayyana tsare-tsarensa ga Najeriya

Shawarar da APC ta ba yan siyasa

Ya jaddada cewa iko daga Allah yake, yana mai cewa duk wanda bai yi nasara ba ya kamata ya nuna haƙuri da bin doka.

Bello ya nuna damuwa kan wasu magoya bayan Adamu da ke ƙona tsintsiya domin nuna rashin amincewarsu da jam’iyyar gabanin zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana cewa kona tsintsiya ba zai rage tasirin APC ba, domin manufofi da nasarorin jam’iyyar ba abubuwa ba ne da za a iya ƙonawa.

A cewarsa, jam'iyyar APC ta samu karɓuwa a Nasarawa ne saboda ayyukan raya ƙasa, zaman lafiya, samar da ayyukan yi da ƙarfafa matasa da mata.

Ya kuma yaba da ayyukan gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa jama'a suna zaɓar ayyuka ne ba tambarin jam’iyya kawai ba.

Mai neman takarar gwamna a APC ta koma SDP a Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa. Hoto: Gov Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Gargadij da APC ta yi wa jama'a

Shugaban APC ɗin ya gargadi jama'a da su guji siyasar rarrabuwar kawuna da wasu ‘yan siyasa ke yi saboda rashin nasara a zaɓe, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

Ya ƙalubalanci masu ƙona tsintsiya da su bayyana irin gudunmawar da suka bayar wa al’umma lokacin da suka samu damar jagoranci a baya.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Lafia, Uba Arikya, ya ce siyasa ya kamata ta mayar da hankali kan kyakkyawan shugabanci da ci gaban rayuwar jama'a.

Shi ma wani jigo na APC a yankin, Sidi Ndagi, ya buƙaci jama'a su zaɓi dukkan ‘yan takarar jam’iyyar daga shugaban ƙasa zuwa sauran mukamai.

Ya yabawa Gwamna Abdullahi Sule kan ayyukan ci gaba da yake yi, tare da roƙonsa ya ci gaba da mayar da hankali kan gina jihar.

Tsohon sufeta janar ya rasa tikitin APC

An ji cewa tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar, ya sha kasa a zaben fitar da gwani na gwamna na APC a jihar Nasarawa.

Mohammed Adamu Abubakar ya nuna rashin gamsuwarsa kan sakamakon zaben wanda ya nuna Sanata Ahmed Wadada ya yi nasara.

Tsohon shugaban 'yan sandan ya nuna cewa zai iya barin jam'iyyar APC idan har ba a saurari kokensa da idon basira ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.