Akalla mutane 10 sun mutu a zanga-zangar #ENDSARS kawo yanzu

Akalla mutane 10 sun mutu a zanga-zangar #ENDSARS kawo yanzu

- Kungiyar Amnesty Internationl ta bayyana adadin matasan da yan sanda suka kashe cikin mako guda

- Tun ranar Alhamis matasa a fadin Najeriya suka fara gudanar da zanga-zanga kan cin zarafin jami'an SARS

- Gwamnatin Buhari ta rusa rundunar SARS kuma ta sanar da maye gurbinta da SWAT

Akalla mutane 10 sun rasa rayukansu a zanga-zangan yunkurin kawo karshen zalunci da cin zarafin da yan sanda ke yiwa yan Najeriya, kungiyar Amnesty International ta bayyana ranar Talata.

Kungiyar kare hakkin bil adaman ta bayyanawa CNN cewa yan sanda na amfani da karfin bindiga wajen cin zarafin matasa masu zanga-zanga tun ranar Alhamis.

"Kawo yanzu, yan sanda sun hallaka akalla mutane 10 tun lokacin da aka fara wadannan zanga-zangar," a cewar Amnesty International.

"Amfani da karfin bindigan da yan sandan ke yiwa yan zanga-zangan ya bayyana yadda jami'an tsaron Najeriya suka dade basu ganin girman rayukan mutane,"

Kungiyar Amnesty ta kara da cewa amfani da karfin bindiga "ba tare da hakki ba laifi ne a idon dokokin duniya."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun yarje a rage farashin lantarki na watanni 3

Akalla mutane 10 sun mutu a zanga-zangar #ENDSARS kawo yanzu
Hakkin mallaka: @HumAngle
Asali: Twitter

A bangare guda, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DCP Frank Mba ya sanar a ranar Talata a Abuja, ya ce duk jami'an 'yan sanda daga yankin kudu maso gabas da kudu-kudu za a horar da su a kwalejin yaki da ta'addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Ribas.

DUBA NAN: Ngige ya ce za a iya la’akari da UTAS a madadin IPPIS wajen biyan Jami’o’i

Wadanda ke rundunar daga arewaci da kuma kudu maso yamma za a horar da su a kwalejin horar da 'yan sanda da ke Nasarawa da ta Ila-Orangun, jihar osun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel