Mutuwar Janar Rabe ya taba tsofaffin sojoji da abokansa, sun kawo mafita
- Tsofaffin hafsoshin soja sun bukaci a yi garambawul ga tsarin tsaron Najeriya bayan mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar,
- Sun ce matsalar ta’addanci, garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ta zama barazana ga kasa baki daya
- Sun kuma bukaci karfafa hukumomin tsaro, horas da masu sa-kai, kafa rundunar masu gadin dazuka, da tallafawa iyalan wadanda rikice-rikice suka shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsofaffin jami’an soja da abokan marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya sun yi wata ganawa a Kaduna.
Abokan nasa sun bukaci a yi cikakken garambawul ga tsarin tsaron Najeriya bayan rasuwarsa sakamakon sace shi da ‘yan bindiga suka yi a Katsina.

Source: Twitter
Tsofaffin jami'an sojojin sun bayyana wannan bukata ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya
Tsofaffin sojoji sun magantu kan mutuwar Rabe
Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi mai ritaya ya yi magana a madadin abokan aiki da iyalan marigayin.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Birgediya Janar Abubakar Abdulqadir mai ritaya, Birgediya Janar M.I. Tsiga mai ritaya, Air Commodore Yusuf Anas mai ritaya da jakadu Ibrahim Usman Gafai da Ahmed Muhammad Musawa.
Abdullahi ya bayyana mutuwar Janar Rabe Abubakar a matsayin babban abin takaici, yana mai cewa lamarin ya nuna yadda matsalar rashin tsaro ke kara muni a sassan Najeriya.
Ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da gwamnatin Katsina da suka taimaka wajen kubutar da matar marigayin, Hajiya Amina Rabe Abubakar, daga hannun masu garkuwa.
Sai dai ya jaddada cewa lamarin ya nuna bukatar daukar sababbin matakai masu karfi domin yaki da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda.

Source: Original
A cewarsa, mutuwar Janar Rabe Abubakar ba wai labari ne kawai ba, illa wata alama ce da ke nuna kalubalen da ke gaban tsarin tsaron kasar.
'Yadda matsalar tsaro ke yaduwa a Najeriya'
Tsofaffin jami’an sun nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ke bazuwa a sassa daban-daban na kasar, tare da gargadin kada a alakanta matsalar da wata kabila ko yanki.
Sun ce ta’addanci, garkuwa da mutane da ‘yan bindiga matsaloli ne na kasa baki daya, don haka suna bukatar hadin kan gwamnati da al’umma wajen magance su.
Abdullahi ya ce wajibi ne a guji siyasantar da matsalar rashin tsaro, domin hakan ba zai taimaka wajen nemo mafita mai dorewa ba, cewar Daily Post.
Kungiyar ta bukaci a karfafa cibiyoyin tsaro, a inganta hadin gwiwar hukumomin tsaro, sannan a kara zuba jari wajen tattara bayanan sirri da kula da iyakoki.
Yadda aka karbo gawar Janar Rabe
An ji cewa an samu bayanai masu karo da juna sun fito kan yadda aka karbo gawar Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) daga wurin 'yan bindiga.
Iyalan tsohon kakakin rundunar soji sun musanta ikirarin cewa Janar Rabe ya rasu ne a sakamakon ciwon sukari da hawan jini.
Babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar sojoji ko Gwamnatin jihar Katsina kan yadda aka dauko gawar marigayin daga daji.
Asali: Legit.ng
