Sojoji Sun Ceto Matar Janar Rabe Abubakar bayan Artabu da ‘Yan Bindiga a Katsina
- Dakarun Operation Fansan Yanma sun ceto matar marigayi Janar Rabe Abubakar bayan wani farmaki da suka kai jihar Katsina
- Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun harbi matar kafin su tsere lokacin da sojoji suka kai masu farmakin a kauyen Tunga
- Rundunar sojojin Najeriya dai ta ce ana ci gaba da farautar ‘yan bindigar karkashin Operation Clean Sweep III a yankin Matazu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Katsina - Dakarun rundunar Operation Fansan Yanma sun samu nasarar ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya bayan artabu da ‘yan bindiga a jihar Katsina.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne karkashin sabon samamen Operation Clean Sweep III a karamar hukumar Matazu.

Source: Twitter
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Katsina
An kaddamar da Operation Clean Sweep III ne bayan sace tsohon babban jami’in sojan tare da iyalansa a yankin, kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.
Majiyoyin sojoji sun sanarwa Zagazola Makama cewa jami’an tsaro sun yi nasarar gano maboyar maharan ne bayan samun bayanan sirri kan inda suke boye.
Rahoton masanin tsaron da ya wallafa a shafinsa na intanet ya nuna cewa dakarun sojoji sun yi arangama da ‘yan bindigar a kauyen Tunga yayin gudanar da aikin ceton.
An ceto matar Janar Rabe Abubakar
A cewar wata majiya daga bangaren tsaro, maharan sun bude wa matar wuta kafin daga bisani su tsere sakamakon matsin lambar da sojoji suka musu.
“Lokacin da muka yi karo da su a kauyen Tunga, sun harbi matar sannan suka tsere saboda matsin lambar da muka sanya musu,” in ji wata majiya.
Majiyar ta kara da cewa an yi wa matar agajin gaggawa a wurin kafin daga bisani aka fara jigilar ta zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Source: Original
An kara tsaurara farautar maharan
Hukumomin soji sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da samame a yankin domin cafke ‘yan bindigar da suka tsere, kamar yadda Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Rundunar sojin Najeriya ta dauki matakin farko bayan mutuwar Janar Rabe a Katsina
Sun ce jami’ai na ci gaba da farautar wadanda ake zargi da hannu a harin da kuma sace marigayi Janar Rabe Abubakar.
A cewar jami’an tsaro, Operation Clean Sweep III zai ci gaba da aiki har sai an tarwatsa dukkan maboyar ‘yan bindiga da sauran cibiyoyin ayyukansu.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da kokarin ganin an kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban doka.
Marigayi Rabe Abubakar ya rasu ne kwanaki bayan sace shi, lamarin da ya jawo damuwa a sassa daban-daban na Najeriya.
An ji wani dalili na mutuwar Janar Rabe
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'daya daga cikin ’ya’yan marigayi Janar Rabe Abubakar, Isyaka Rabe, ya yi watsi da ikirarin da Gwamnatin Katsina a kan ajalin mahaifinsa.
Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga gwamnatin jihar Katsina da ya ce Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya ya mutu ne sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini.
Isyaka Rabe ya ce marigayin ba shi da tarihin fama da ciwon sukari ko hawan jini a rayuwarsa, sabanin yadda gwamnati ta yi iƙirari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
