Rarara Ya Fadi Dalilin da Yasa ba zai Yi wa Davido Martani da Turanci ba

Rarara Ya Fadi Dalilin da Yasa ba zai Yi wa Davido Martani da Turanci ba

  • Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi bayani game da jingina masa rashin ilimi da Davido ya yi a cikin wata takaddama da suka yi
  • Rarara ya bayyana cewa shi ba jahili ba ne domin a tarihin karatun da ya yi ya taba rike almajirai masu karatun Al-Kur'ani mai girma
  • Mawakin ya kuma yi magana kan masu cewa ya kamata ya yi wa Davido martani cikin harshen Turanci lura da cewa ba ya jin Hausa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Dauda Kahutu Rarara ya kare kan shi game da zargin da Davido ya masa na cewa ba shi da ilimi balle ya yi magana da shi.

Kahutu Rarara ya kara da cewa yawancin mutane ba su fahimci cewa ilimi shi ne aiki da hankali ko kuma yin abin da a dace ba.

Kara karanta wannan

Bayan Davido, Rarara ya dura kan malaman Arewa masu wa'azi kan rashin tsaro

Davido tare da Dauda Kahutu Rarara
Dauda Rarara a hagu tare da Davido a dama. Hoto: Dauda Kahutu Rarara|Davido
Source: Facebook

Rarara ya yi martani ne a wata hira da DCL Hausa ta wallafa a Facebook, inda ya yi karin bayani kan dalilin kin yi wa Davido magana da Turanci.

'Ni ba jahili ba ne,' Dauda Rarara

A wani martani da Davido ya yi wa Rarara a shafinsa na X, ya bayyana cewa ba zai yi wa Dauda Kahutu magana ba saboda ba shi da ilimi.

Sai dai Rarara ya bayyana cewa shi mai ilimi ne:

'Na riga na raina wayon Davido, da ina ganin girman shi, tun da har bai san darajar Najeriya ba.
"Ni ban san ilimin da ya ke magaba a kai ba. Bakin gwargwado dai ilimin nan na yi. A cikin masu ilimi ma bakin gwargwado ni mai ilimi ne.
"Domin na taba rike almajirai. Domin na kusa kai gardi kafin na bar karatun allo, ko kuma in ce na kai gardi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya yi magana kan kama dan ta'adda Bello Turji

Rarara ya kara da cewa duk wanda ya kai gardi a Arewacin Najeriya ba za a taba ce masa ba shi da ilimi ba ko a ce shi jahili ne.

Magana kan kin yin Turanci

Bugu da kari, Rarara ya bayyana cewa wasu za su dauka cewa magana da Turanci ne kawai ilimi amma sam ba haka ba ne.

"Ba ni da wani yare da ya wuce Hausa, duk abin da zan yi dan Hausa zan yi shi, da Hausa nake yi. Maganar Turanci kuma za ka iya zuwa ka koya."

Rarara ya ce Davido ya tashi a matsayin Bayerabe shi kuma ya tashi a Bahaushe, kamar yadda ba zai bar Yarbanci ba shi ma ba zai daina Hausa ba.

Davido sanye a wajen wasan kofin duniya
Davido sanye da rigar da ta jawo Rarara ya yi magana. Hoto: Davido
Source: Facebook

Rarara ya yi magana ga malamai

A wani labarin, mun kawo muku cewa Dauda Kahutu Rarara ya yi kira ga malaman addinin Musulunci a kan yawan magana kan rashin tsaron da ya addabi kasar nan.

Rarara ya ce ya kamata malamai su fito karara su yi magana ga matasa masu yada bidiyon 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane a intanet.

Ya ce hakan na cikin manyan matsalolin Arewacin Najeriya amma abin haushi ne yadda masu malaman da kansu suke yada irin maganganun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng