Jerin Sunaye: Kusoshin Gwamnatin Buhari 5 da Yanzu Suka Yi Tsit Kamar Basa Nan

Jerin Sunaye: Kusoshin Gwamnatin Buhari 5 da Yanzu Suka Yi Tsit Kamar Basa Nan

Zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman zama tarihi, ta fuskar jin amo, ba don komai ba sai duba da yadda yanzu batu kanta ya yi kasa, duk kuwa da yadda a baya ta kowane yanki ake jin amon ta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Yayin da ludayin sa ke kan dawo, ana ganin cewa akwai wasu mutane wadanda suka kewaye Buhari, kuma suka zama masu karfin fade aji a gwamnatinsa, wasu lokutan ma ake ganin kamar sune ke sarrafa kasar.

A wannan karon Legit Hausa ta zakulo muku wasu mutane biyar, wadanda suka sha sharafinsu a baya, yanzu kuma ambatonsu yayi kasa, kwata kwata aka daina jin amonsu, ba a iya shafukan sada zumunta ba, har da kusan bakunan mutane baki daya.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
Jerin Sunaye: Kusoshin gwamnatin 5 Buhari da yanzu suka yi tsit kamar basa nan Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Wadannan mutane kuwa sun hada da yan’uwan shugaban kasar, Ministoci, Sanatoci da gwamnoni ma baki daya.

Kara karanta wannan

Ba kamar Buhari ba, Tinubu ya dauki mataki kan yawan kashe kudade a tafiye-tafiye, ya fadi dalili

1. Aisha Buhari

Ita ce matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadda kuma ta taka rawa wajen kwatarwa mata da kananan yara yanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aisha Buhari ta kuma yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin mijin nata kan wasu manufofi da ya bujiro da su.

Kazalika matar tsohon shugaban kasar yar boko ce domin kuwa har wani littafi na turanci ta wallafa mai suna, "Essentials of Beauty Therapy: A Comprehensive Guide for Beauty Specialists."

Bayan karewar wa’adin mulkin mijin nata ne kuma sai ta yi kaura zuwa Landan domin samun digiri na uku a jami’ar Westminster.

2. Rotimi Amaechi

Wannan shi ne tsohon gwamnan jihar Ribas, kuma tsohon ministan Sufuri na tarayya sannan daya daga cikin masu fada aji a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Buhari.

Rotimi ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tsarin sufurin jirgin kasa da bunkasa bangaren sufuri na ruwa da ma bangaren sufurin jiragen sama a kasar.

Kara karanta wannan

Jerin Hukumomin Gwamnati Da Suka Bada Kyauta Ga Matar Da Ke Tashi 4.50 Na Asuba Don Yi Wa Mijinta Girki

Ya kuma rike manyan mukamai a jamiyyar APC mai mulki, sannan shine babban daraktan yakin neman zaben tsohon shugaban kasar a zabukan 2015 da 2019.

A 2022, ya yi murabus a matsayin minista don neman takarar shugaban kasa a APC. duk da kokarinsa, ya zo na biyu a zaben fidda gwanin jam'iyyar, inda ya sha kaye a hannun Tinubu.

3. Abubakar Malami

Tsohon ministan shari’a na tarayyar Najeriya, ya kasance mai kyakkyawar alaqa da jamiyyar APC, ya kuma taka rawar gani sosai wajen nasarar jam'iyyar a 2015 da 2019.

Tsohon shugaban kasar ya nada Malami a matsayin ministan shari’a a shekarar 2015 tare da sake sabunta nadin nasa a 2019.

Kuma yayin da yake kan kujerarsa ya taka rawa sosai wajen shiga shari’o’i da dama wadanda suka kunshin gwamnatin tarayya.

Malami ya taka rawa wajen farfado da tsarin shari’a a Najeriya, sannan daya daga cikin masu fade aji zamanin mulkin tsohuwar gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

'Ba zan lamunci rashin nasara daga gareku ba', Tinubu ya kyankyasa gargadi ga manyan sojojin kasa

4. Ibikunle Amosun

Ya kasance tsohon gwamnan jihar Osun kuma sanata sau biyu, wanda ya taka rawa muhimmiya mai tarin yawa ga ci gaban gwamnatin Buhari.

Amosun ya kuma taka rawar gani wajen kawowa jamiyyar APC yankin Kudu maso Yamma a zabukan 2015 da 2019.

Baya ga gudunmawar da ya bayar a bangaren siyasa, ya kuma tsaya rsayin daka wajen ganin an samar da tarin ayyukan more rayuwa a jihar Ogun da suka hadar da gina gadoji, makarantu, asibitoci da sauransu.

Bayan ya kammala wa'adin mulkinsa na biyu, a jihar, ya koma a matsayin sanata wanda har ta kai ga shi ga rike mukamin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan bunkasa kasuwanni.

5. Tunde Sabi’u

Dan’uwa kuma babban mataimaki na musamman ga Buhari na daga cikin mutane masu fada aji a gwamnatin tsohon shugaban kasar, kuma ana zargin yana daga cikin dan gaba goshi kuma dan komai da ruwana a harkar tafiyar da Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan cewa bai son a kai masa ziyara, Buhari ya yi kyautar galleliyar mota ga dan a mutunsa

Yawancin kwangiloli da aka bayar a zamanin tsohon shugaban kasar, ya na da hannu wajen fitar ta, kuma an nada shi a a matsayin mataimakin daraktan hukumar NIA.

Bayan saukar Buhari daga mulki an kama Tunde bisa zargin mallakawa kansa wasu makamai ba bisa kaida ba.

Duk da cewa an bayar da belinsa, daga baya jami’an tsaro sun sake kama shi a wajen harabar kotun. A halin yanzu dai ana ci gaba da shari'arsa.

Buhari ya yi kyautar galleliyar mota

A wani labarin, mun ji cewa tsohon shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya gwangwaje wani dattijo da kyautar mota a ranar Asabar 6 ga watan Janairun 2024.

Wannan kuwa ya faru ne a lokacin da dattijon ya kai masa ziyara a gidansa da ke Daura, kamar yadda tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel