Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Naira Miliyan 50, Za a Tallafawa Masu Fama da Cutar Daji

Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Naira Miliyan 50, Za a Tallafawa Masu Fama da Cutar Daji

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da asusun N50m domin tallafa wa masu cutar daji da ke fama da matsalolin rayuwa yayin jinya
  • Sama da marasa lafiya 600 ne suka nemi tallafin, yayin da aka tantance fiye da mutum 200 da za su fara amfana da shirin yanzu
  • Duk wanda aka tantance zai karbi akalla N100,000 domin rage nauyin sufuri, masauki da sauran bukatu a yayin da yake jinyar wannan cuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da asusun Naira miliyan 50 domin tallafa wa masu fama da cutar daji, musamman wadanda ke fuskantar matsalolin tattalin arziki da ke hana su samun cikakkiyar kulawar lafiya.

Karamin ministan lafiya da walwalar jama'a, Dakta Iziaq Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin bikin kaddamar da rabon kudaden tallafin a Abuja.

Kara karanta wannan

N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da tallafin N50m ga masu fama da cutar daji
Karamin ministan lafiya, Dakta Iziaq Salako da ya kaddamar da tallafin N50m ga masu cutar daji. Hoto: @SalakoIziaq
Source: Twitter

Za a tallafawa masu kansa da N50m

Salako ya ce an kirkiro asusun ne domin taimaka wa marasa lafiya wajen shawo kan matsalolin da ba na magani ba, kamar kudin sufuri, masauki, abinci da kuma rashin goyon bayan iyali, in ji rahoton Punch.

Karamin ministan ya bayyana cewa irin wadannan matsaloli na hana mutane da dama fara jinya ko kuma kammala maganin da ake yi musu.

A cewarsa, sama da mutum 600 da ke fama da cutar daji sun riga sun gabatar da bukatar neman tallafi a karkashin shirin, kuma an amince da bukatar sama da mutum 200.

Ministan ya ce an tantance fiye da mutum 200 bayan wani tsari na bincike da ya hada da daraktocin asibitoci da likitocin da ke kula da su.

Ya kara da cewa duk wanda aka tabbatar ya cancanta zai karbi akalla N100,000 domin rage wasu daga cikin matsalolin da ke tattare da jinyar cutar daji.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Za a tura kudin kai tsaye ga marasa lafiya

Ministan ya ce za a rika tura kudaden kai tsaye ga wadanda suka cancanta domin tabbatar da gaskiya da kuma kauce wa duk wata matsala a tsarin rabon tallafin.

Ya bayyana cewa duk da irin kokarin da gwamnati ke yi wajen fadada cibiyoyin kula da masu cutar daji da rage kudin magani, har yanzu marasa lafiya da dama na fuskantar kalubalen da ke hana su samun kulawa yadda ya kamata.

Salako ya ce kudin zirga-zirga, neman masauki a biranen da ake da cibiyoyin kula da cutar daji, karancin abinci da rashin tallafin iyali na daga cikin abubuwan da ke janyo jinkirin jinya.

Akalla masu fama da cutar daji 200 ne aka fara tantancewa don amfana da tallafin N50m
Karami ministan lafiya ya mika tallafi ga masu fama da cutar kansa. Hoto: @TemiyemiSherif
Source: Twitter

Yadda aka samar da shirin

A cewar ministan, an samar da wannan shiri ne bisa shawarar kwamitin fasaha na Tsarin Yaki da Cutar Daji na Kasa na shekarun 2026 zuwa 2030, kamar yadda rahoton Independent ya nuna.

Ya yaba wa mambobin kwamitin bisa kishin kasa da sadaukarwar da suka nuna, inda ya bayyana cewa wasu daga cikinsu sun bayar da gudunmawar miliyoyin naira daga aljihunsu domin fara asusun.

Kara karanta wannan

Dakarun gandun daji: Tinubu amince a dauki sababbin ma'aikata 1,000 a Katsina

An samar da rigakafin cutar daji

A wani labari, mun ruwaito cewa, bayan shafe shakara da shekaru, masana kimiyya a Rasha sun samar da sabon rigakafin cututtukan daji mai suna "Enteromix".

Maganin rigakafin ya dogara ne da fasahar mRNA, wadda aka yi amfani da ita a wasu mgungunan rigakafin COVID-19.

An ce gwajin farko ya nuna cewa maganin yana rage girman cutar daji da kuma inganta tsawon rayuwar masu fama da cutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com