Sarki Charles III Ya Kamu Da Cutar Daji, Bayanai Sun Fito

Sarki Charles III Ya Kamu Da Cutar Daji, Bayanai Sun Fito

  • Fadar Buckingham ta ce gwaje-gwajen da aka yi a asibiti a baya-bayan nan sun nuna Sarki Charles ya kamu da wata na'uin cutar kansa
  • Likitoci sun bai wa Sarki Charles shawarar cewa ya dage duk wani aiki da ya shafi fita bainar jama'a yayin da aka fara masa magani a yau
  • Sai dai, Sarkin na Birtaniya, zai cigaba da yin ayyukansa na kasa da dubawa da sa hannu kan takardu kamar yadda ya saba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Landan, Birtaniya - Likitoci sun gano cewa Sarki Charles III ya kamu da wata na'uin cutar daji yayin da ake masa maganin lalurar mafitsara.

A cewar fadar ingila ta Buckingham, an fara yi wa Sarki Charles magani, inda likitocinsa suka bashi shawarar jingine duk wasu ayyuka da sai ya fita bainar al'umma.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Sarki Charles ya kamu da cutar kansa
Fadar Buckingham ta ce Sarki Charles ya kamu da cutar daji. Hoto: @RoyalFamily
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Sarki Charles III zai cigaba da yin ayyukan da suka shafi kasa da rattaba hannu kan takardu na yau da kulum.

"Yayin da ake yi wa Sarkin magani na lulurar mafitsara da ta fara kumbura, an gano wata matsalar daban. Binciken da aka yi na nuna nau'in cutar daji ne.
"Mai martaba ya fara karbar magani, inda likitocinsa suka bashi shawarar ya jingine ayyukan da suka shafi fita bainar jama'a. A yayin da ya ke karbar magani, mai martaba zai cigaba da yin ayyukan kasa da rattaba hannu kan takardu."

Da ake bayani kan dalilin da yasa aka bayyana abin da ke damunsa, wani sashi na sanarwar ta ce:

"Mai Martaba Sarkin ya zabi ya bayyana cutar da ke damunsa don hana hasashe kuma da fatan hakan na iya taimakawa jama'a fahimtar duk wadanda ke fama da cutar kansa a duniya."

Kara karanta wannan

Uwar gidan Shugaba Tinubu ta yi ƙus-ƙus da matan gwamnoni a Aso Villa, bayanai sun fito

Sarki Charles ya godewa likitocinsa saboda daukan mataki cikin gaggawa kuma yana fatan nan bada dadewa ba zai cigaba da ayyukansa kamar yadda ya saba.

An kuma sanar a shafin X na @RoyalFamily, a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu.

An Kwantar Da Sarki Charles a Asibiti

A baya-bayan nan ne kuka ji cewa an kwantar da Sarkin Birtaniya, Charles III a asibiti mai zaman kansa a Landan, a ranar Juma'a don yi masa tiyata saboda matsalar mafitsara.

Fadar Buckingham ta rahoto cewa rashin lafiyar Sarki Charles ta tsananta amma a ranar Juma'a ta ce ya samu sauki yayin da ake shirin yi masa tiyatan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel