Ciwon daji ko kuma cutar kansa a takaice
Ciwon daji ko kuma kansa wata cuta dake janyo gurbacewar ƙwayoyin halittu a jikin dan Adam, wadda take yaduwa daga sashe zuwa sashe tare da karya duk wata kafa da ta shiga.
Kadan daga cikin alamomi da mutum zai gane yana dauke da cutar kansa sune; yawan tari ma tsayi, zubar da jini ba tare da wani dalili ba, bayyanar tsuro tamkar ƙari ko maƙoƙo a jikin mutum, ramewar jiki da yawan kasala, sai kuma yawan ciwon ciki.
Hasashe ya bayyana cewa, sigari itace kan gaba wajen haifar da cutar kansa, kana teba, rashin cin lafiyayyen abinci, da kuma rashin motsa jiki ke take mata baya.
A shekarar 2015 da ta gabata, akwai kimanin mutane miliyan 90.5 dake dauke da cutar, inda ƙiyasi ya bayyana cewa ana samun mutane miliyan 14.1 a duk shekara dake kamuwa da cutar, baya ga miliyan 8.8 dake mutuwa duk shekara a sakamakon cutar.
Mafi akasari dai, wannan cuta ta kan kama sassan jiki da suka hadar da; huhu, mahaifa, mama da kuma fata. Akwai kuma mafi hatsarin ta dake kama jini da kuma ƙwaƙwalwar dan Adam, inda hakan yafi afkuwa a nahiyyar Afirka.
KARANTA KUMA: Kasashe biyar sun kulla yarjejeniyar jiragen sama da shugaba Buhari
Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, kaso 90 zuwa 95 cikin 100 suna kamuwa ne da cutar a sakamakon al'amurran zamantakewar su, inda ragowar kaso 5 zuwa 10 ke kamuwa da cutar a sakamakon gado tun daga iyaye da kakanni.
Kwarrarun likitoci sun bayyana cewa, masu ribatar abincin mai lafiya, ƙauracewa barasa da sigari, tare da motsa jiki, cutar ta kan samu wahalar shiga jikin su, wadda idan akwai ta kuma ba ta wani tasiri na a zo a gani.
A baya jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai illoli da dama da lemun tsami ya ƙunsa muddin aka ribaci yawaitar ta'ammali da shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng