Tsaro: An Kafa Zafafan Dokoki a Katsina, an Hana POS, Cajin Waya da Sauransu
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya dauki sababbin matakai domin inganta tsaro da magance matsalar 'yan bindiga masu sace jama'a
- Lamarin ya biyo bayan matakan da hukumomi suka ce za su dauka bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar (Mai ritaya) a hannun masu garkuwa a jihar
- Daga cikin matakan tsaro da gwamnati dauka akwai hana sana'ar POS da cajin waya a wasu kananan hukumomin jihar da rashin tsaro ya yi kamari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya fitar da sabon umarni da nufin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar, musamman a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Gwamnan ya sanar da matakan ne bayan wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar tare da hukumomin tsaro, shugabannin gargajiya, da muhimman masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan
Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamna Dikko Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne bayyana matakan da aka dauka a wani sako da ya fitar a Facebook.
Matakan tsaro da Katsina ta dauka
Gwamnatin Katsina ta sanar da cewa ta haramta sayarwa, saye, safara da ajiyar man fetur a cikin jarkoki a duk faɗin jihar nan take.
Ta ce"
"An ɗauki wannan matakin ne domin hana karkatar da man fetur zuwa hannun masu aikata laifuffuka da ke ta'addanci a yankunan karkara."
Gwamnan ya kuma amince da rufe harkokin POS da wuraren cajin wayoyin hannu na kasuwanci a kananan hukumomin Matazu da Musawa nan take.
Gwamnatin Katsina ta kafa hujja da cewa:
"Binciken tsaro ya nuna cewa ana amfani da waɗannan wurare ta hanyar da ke taimaka wa ƙungiyoyin masu laifi wajen gudanar da ayyukansu."
Bugu da ƙari, an haramta amfani da babura a dukkan Kananan hukumomin Matazu da Musawa:

Kara karanta wannan
Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito
"An sanya wannan takunkumin ne domin katse zirga-zirga da ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane waɗanda galibi ke dogaro da babura wajen sufuri."

Source: Facebook
Muhimmancin tsaro a Katsina
Gwamna Radda ya bayyana cewa tsaron al’umma shi ne babban abin da gwamnatinsa ta saka a gaba, tare da tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro.
Ya yi kira ga al’umma da su mara wa hukuma baya ta hanyar bin umarnin ta tare da bayar da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro duk lokacin da ya zama dole.
Dikko Umaru Radda ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba za ta sassauta wa duk wanda ya saɓa wa sababbin dokokin ba.
An ceto matar Janar Rabe
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun sojojin Najeriya sun sanar da cewa sun ceto matatar marigayi Janar Rabe Abubakar a Katsina.
A kwanakin baya ne wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya a jihar.
Sojojin Najeriya sun kutsa daji domin ceto matar biyo bayan rasuwar tsohon sojan a hannun 'yan ta'addan da suka yi garkuwa da shi.
Asali: Legit.ng