Masifa Ta Fada Amurka, Jirgin Soji Ya Fado, Jama'a da Sojoji Sun Mutu
- Jirgin yakin Amurka ya yi mummunan hadari bayan tashi daga wani sansanin soji da yammacin ranar Litinin, 15 ga Yunin 2026
- Rahotanni daga hukumomi sun tabbatar da cewa jirgin ya lalace kuma kusan mutum 10 da ke cikin shi sun riga mu gidan gaskiya
- Wani rahoto ya nuna cewa jirgin da ya fado na daga cikin samfurin jiragen da Amurka ta yi amfani da su wajen kai hare-hare Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Mutane takwas sun mutu bayan wani jirgin yaƙi na rundunar sojin saman Amurka kirar B-52 ya faɗi nan take bayan tashinsa daga sansanin sojin sama na Edwards da ke Kudancin California.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:20 na safe agogon yankin a ranar Litinin yayin da jirgin ke gudanar da aikin gwaji na yau da kullum.

Source: Getty Images
Hayaki ya tashi bayan hadarin jirgi
BBC ta rahoto cewa hatsarin ya haddasa wani babban hayaki baƙi da ya tashi sama wanda ake iya gani daga nesa daga wajen da abin ya faru.
“A yau, Sansanin Sojin Sama na Edwards ya fuskanci wata mummunar masifa, kuma mun rasa manyan Amurkawa takwas,”
In ji Kanal James Hayes, yana bayyana wadanda ke cikin jirgin a matsayin
"Tawaga ta sojoji, ma’aikatan gwamnati da kuma 'yan kwangila.”
Munin hadarin jirgin sojin Amurka
Tun da farko, sansanin ya bayyana cewa alamun farko sun nuna cewa hatsarin ba zai yiwu a tsira daga gare shi ba.
Bayan nazarin bidiyon farko na hatsarin, Kanal Hayes ya tabbatar da cewa lamarin:
“Hatsari ne da ba za a iya ceto jirgin ba kuma babu wanda zai iya tsira,”
Hayes ya ce ana sanar da iyalan mamatan, kuma za a bayyana sunayensu sa’o’i 24 bayan kammala tattara bayanan farko.
Ya ce hatsarin ya kasance a cikin yankin sansanin sojin sama na Edwards a kan titin tashin jirage, kuma an dakatar da ayyukan sansanin na ɗan lokaci.

Source: Getty Images
Ba a gano dalilin hadarin ba
Hukuma ta ce har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba, kuma ba za a iya yin hakan ba sai bayan wasu bincike da za su iya ɗaukar kwanaki 30.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Gwamnan California, Gavin Newsom, ya bayyana hatsarin a matsayin abin takaici mai muni tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu.
Jirgin B-52 jirgin yaƙi ne mai dogon zango da ake amfani da shi wajen kai hare-haren bam, kuma yana cikin jiragen da suka halarci hare-haren bam a lokacin yaƙin da Amurka da Isra’ila suka yi da Iran.
Ga bidiyon hadarin da ABC ta wallafa a X:
Amurka ta yi sulhu da Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa sun cimma yarjejeniya da Iran kan tsayar da yaki.

Kara karanta wannan
Jirgin sama dauke da sojoji ya yi mummunan hatsari, dakaru 5 sun bakunci lahira a India
Trump ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Yunin 2026 bayan shafe tsawon lokaci ana gwabaza yaki a Gabas ta Tsakiya.
A daya bangaren, gwamnatin Iran ta tabbatar da cimma yarjejeniyar tare da bayyana cewa akwai abubuwan da za su biyo baya a nan gaba.
Asali: Legit.ng

