An Kuma: Amarya Ta 'Hallaka' Mijinta a Kano kan Sabani game da zuwa 'Party'

An Kuma: Amarya Ta 'Hallaka' Mijinta a Kano kan Sabani game da zuwa 'Party'

  • Kotun Majistare a Kano ta tsare wata mata bayan zargin hallaka mijinta bayan samun sabani wanda ya jawo nadama
  • Yan sanda sun zargi Khadija da daba wa mijinta wuka a kirji da wuya yayin da yake barci a kan kujerar dakinsu
  • Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa 8 ga Satumba, yayin da ake jiran shawarar lauyoyin gwamnati kan matakin da za a ɗauka na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin tsare wata sabuwar amarya, Khadija Sa’idu, a gidan gyaran hali saboda zargin aikata kisan kai.

Alƙalin kotun, Haulatu Magaji Kankarofi, ya bayar da umarnin tsare matar ne bayan ‘yan sanda sun gurfanar da ita kan zargin daba wa mijinta wuka.

Amarya ta hallaka mijinta a Kano
Taswirar jihar Kano da ake yawan samun kashe-kashe tsakanin ma'aurata. Hoto: Legit.
Source: Original

Ana zargin Khadija, wadda ke zaune a Hayin Lawal, Rimin Kebe, Kumbotso, da kai wa mijinta, Malam Auwal Adam, hari a gidansu, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba da mace ta yi yunkurin kai harin bam a ginin majalisar Amurka

An yi auren gata a Kano

Wannan lamari na zuwa ne kwanai kadan bayan gudanar da bikin auren gata a Kano wanda ke tallafa wa maza da mata da ke bukatar aure kuma ba su da hali.

A kwanakin baya ne, gwamnatin Kano ta amince da fitar da Naira miliyan 300 domin tallafa wa shirin auren gata da Hukumar Hisbah ke gudanarwa.

Kowace amarya za ta samu Naira 200,000 a matsayin jari da sadaki, yayin da sabbin ma’aurata za su samu kayan daki.

Wasu masu sharhi sun fara zargin dalilin da ya sa ake samun yawan kashe-kashe tsakanin ma'auarata suna alakanta shi da auren gata saboda arahar shi.

An tsare mata da ta kashe mijinta a Kano
Sufeta-janar na yan sanda a Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Abin da ya jawo rigima tsakanin mata da miji

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan amaryar ta nemi izinin mijinta domin zuwa wata kasaitacciyar liyafa, amma ya ƙi amincewa da bukatarta.

Lauyan masu gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa bayan rashin jituwar, Khadija ta daba wa mijinta wuka a kirji yayin da yake barci.

Kara karanta wannan

Mahaifi ya kona 'yar cikinsa saboda malalar fitsarin kwance kullum a gadonsu

An kuma zargi matar da kai masa wasu raunuka a wuya yayin harin da ake zargin ta kai masa a gidansa.

Kotun ta ji cewa an garzaya da Auwal zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa sakamakon raunukan da ya samu.

A zaman kotun na ranar Alhamis, mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa ana jiran shawarar doka daga lauyan gwamnatin jihar domin sanin matakin gaba.

Alƙalin kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga Satumba domin sake gabatar da batun a gaban kotu, kamar yadda Sahara Reporters ta ce.

Amarya ta yanka wuyan ango a Kano

Mun ba ku labarin cewa ana zargin wata amarya da ba a wuce watanni biyu da aurenta ba, ta kashe mijinta a unguwar Rimin Kebe da ke Jihar Kano.

Ganau da lamarin ya auku a kan idonsu sun ce matar ta yanka makogwaron angonta yayin da sabanin ya shiga tsakaninsu.

Dakarun rundunar ’yan sanda sun garzaya wurin bayan samun rahoto, kuma an ce sun kama matar da ake zargi domin ci gaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.