Jira Ya Kare: An Fitar da Sanarwa kan Daukar Ma'aikatan Hukumomin NSCDC, NIS, NcoS da Fire Service
- Hukumar CDCFIB ta ce za ta kammala daukar sababbin ma’aikatan hukumomin NSCDC, NIS, NCoS da Fire Service cikin makonni hudu
- Ta bukaci masu neman aikin da su yi haƙuri tare da guje wa masu neman kuɗi da sunan daukar ma’aikata
- Dubban matasa sun shafe tsawon lokaci suna jiran sakamakon daukar ma’aikatan hukumomin guda hudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar CDCFIB ta yi magana kan daukar ma'aikatan Hukumar Tsaron Farar Hula ta Najeriya (NSCDC), Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS), Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS).
Hukumar CDCFIB ta ce za ta kammala aikin daukar ma’aikatan hukumomin tsaro guda hudu da aka dade ana jira, cikin makonni hudu masu zuwa.

Source: Twitter
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren hukumar, Manjo Janar ma ritaya A. M. Jibril, ya sanya wa hannu ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026 kuma aka wallafa a shafin X.
Dalilin jinkiri kan daukar ma'aikatan
Sanarwar ta zo ne bayan dogon lokaci da dubban matasa marasa aikin yi suka shafe suna jiran kammala aikin daukar ma’aikatan da ya shafi wadannan hukumomi hudu.
CDCFIB ta ce yawan mutanen da duka cike daga sassa daban-daban na kasar ya sa aka bukaci gudanar da cikakken tsarin tantancewa domin tabbatar da adalci da sahihancin aikin.
Hukumar ta ce ba za ta yi gaggawar kammala aikin ta hanyar rashin adalci ba, amma ta tabbatar da cewa tsarin ya shiga matakansa na karshe.
CDCFIB ta kwantar da hankulan matasa
A cewarta, za a kammala daukar aikin cikin makonni hudu, sannan a sanar da wadanda suka yi nasara ta hanyar shafin daukar ma’aikatan na hukuma.
“An gudanar da aikin daukar ma’aikatan, kuma yanzu ya shiga matakansa karshe, wanda za a kammala cikin makonni hudu,” in ji hukumar.
CDCFIB ta bukaci masu neman aikin da su ci gaba da hakuri tare da sanya ido kan shafin daukar ma’aikatan na hukuma domin samun sahihan bayanai.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Ruwan koguna na shirin ɓallewa ya afka cikin Kaduna, Jigawa da wasu jihohi
An gargadi wadanda suka cike aikin
Hukumar ta kuma gargadi masu neman aikin da su yi hattara da mutane ko shafukan da ke neman kuɗi ko kuma ikirarin cewa suna da damar ganin jerin sunayen wadanda aka dauka ba tare da an sanar da su a hukumance ba.

Source: Twitter
Wani mai neman aikin, Hamza Kabir, ya shaida wa Legit Hausa cewa dogon jinkirin ya sa ya fara rasa kwarin gwiwa kan tsarin daukar sababbin ma'aikatan hukumomin guda hudu.
Ya ce jinkirin ya kara masa damuwa da rashin tabbas, musamman saboda aikin na daga cikin manyan damar da matasan Najeriya ke nema domin samun aiki domin dogaro da kai.
Gwamnatin Tinubu za ta dauki malamai
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara aikin ɗaukar malamai 3,252 na ƙungiyoyin iyaye da malamai (PTA) aiki a gwamnatin tarayya.
A cewar fadar shugaban kasa, wannan zai magance matsalar ƙarancin malamai a Kwalejojin Unity da Kwalejojin Fasaha na gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng
