Zaben Osun: Davido Ya Je har Gidan Wike Ya Ce Sun Kifar da APC
- Fitaccen mawaki, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi wata muhawara ta raha da Ministan Abuja, Nyesom Wike a gidansa
- Davido ya maimaita cewa “na yi nasara, na doke ku” yayin da yake musayar barkwanci da Wike a wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta
- Lamarin ya faru ne yayin da Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ziyarci Wike a Abuja ranar Alhamis, bayan nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi wata musayar barkwanci da Ministan Abuja, Nyesom Wike, inda ya yi ikirarin cewa ya doke bangaren ministan a zaben Osun.
Faifan bidiyon musayar maganar da ya bazu a ranar Juma'a, ya nuna Davido cikin kayan gargajiya masu launin ruwan kasa yana tsaye a gaban Wike.

Source: Facebook
Me Daido ya ce wa Wike?
Punch ta wallafa cewa Davido ya, cewa Wike “Na yi nasara. Na doke ku,” yayin da Wike, wanda ke zaune cikin farar riga, yake musanta maganar cikin fara'a.
Wike ya ce, “A'a, a'a,” amma Davido ya sake jaddada cewa, “N yi nasara! Na doke ku.”
Davido ya yi raha da Wike
A yayin da Wike ya tambaye shi, “Ka doke mu?”, Davido ya sake cewa, “Na doke ku,” yana mai jaddada cewa shi ne ya yi nasara.
Wasu daga cikin mutanen da ke wurin sun shiga cikin hirar da kalmar “a bari haka ”, lamarin da ya kara sanya dariya a dakin.
Daga bisani, Davido ya durƙusa a gaban Wike, sannan ya tashi ya rungume shi, abin da ya jawo tafi, ihu da dariya daga mutanen da ke wurin.
Ziyarar Adeleke ga Wike
Vanguard ta ruwaito cewa Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ziyarci Wike a Abuja a wani bangare na ganawa da wasu masu ruwa da tsaki bayan sake zabensa a matsayin gwamnan jihar.
Wani hoton da mai taimaka wa Wike kan harkokin yada labarai, Lere Olayinka, ya wallafa ya nuna Adeleke da ministan suna rike da takardar shaidar nasarar zaben gwamnan.

Source: Twitter
Kafin ziyarar Wike, Adeleke ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Adeleke, wanda ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar Accord, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 511,067.
Ga bidiyon da Omoyele Sowore ya wallafa a X:
Maganar da Wike ya yi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Wike ya bayyana cewa Ademola Adeleke ya samu nasarar lashe zaben Osun ne saboda Shugaba Bola Tinubu ya ba da damar gudanar da zaben cikin 'yanci da adalci.
Legit Hausa ta rahoto cewa Wike ya musanta zargin cewa gwamnatin tarayya ta yi amfani da karfinta wajen karkatar da zaben zuwa ga APC.
Ya ce Tinubu ya bar tsarin dimokuradiyya ya gudana yadda ya kamata, yana mai cewa da shugaban kasar yana son amfani da karfin gwamnatin tarayya wajen lashe zaben, da sakamakon ya kasance daban.
Asali: Legit.ng
