Yan Bindiga Sun Far Wa Mutane bayan Sun Dawo daga Sayayyar Kayan Sallah a Jihar Katsina
- Yan bindiga sun far wa mutanen kauyuka biyu bayan sun daga kasuwa a yankin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina
- Mazauna yankin sun ce wadanda aka kashe sun dawo ne daga kasuwar mako-mako da ke ci a garin Guga, inda suka yi sayayyar Sallah
- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta ce za ta fitar da sanarwa kan abin da ya faru nan ba da jimawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - 'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 11, ciki har da jami'in tsaro da mace mai juna biyu, yayin da suka kai hari kan wasu ƙauyuka biyu a karamar hukumar Bakori, jihar Katsina.
Harin ya faru ne a ranar Lahadi da tsakar rana a ƙauyukan Gidan Wawu da Gidan Sarkin Noma, waɗanda maƙwabtan juna ne a karkashin gundumar Guga.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kashe mutum 11
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa yan bindigar sun kai harin ne a daidai lokacin da mazauna garin ke dawowa daga Kasuwar Guga ta mako-mako.
Wani mazaunin yankin, Mahadi Danbinta Guga, ya bayyana cewa maharan sun farmaki ƙauyukan a ranar kasuwa, lokacin da mutane suka koma gida bayan sun je sayayyar babbar Sallah.
"Mutane sun dawo daga kasuwa suna gida lokacin da aka kai musu hari aka kashe su," in ji shi.
Barnar da yan bindiga suka yi a Katsina
A cewar mazauna garin, maharan sun kashe mutane 11, sun ƙona gidaje, sun lalata kayayyaki, sannan sun kwashe dabbobi kafin su tsere daga yankin.
Daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su akwai Mujitafa Nuhu, wanda aka fi sani da “Officer,” mamba ne a rundunar tsaron sa-kai ta jihar wato KSWC, wadda ke tallafa wa jami'an tsaro.
Mazauna garin sun kuma tabbatar da cewa akwai mace mai juna biyu cikin waɗanda aka kashe, ko da yake har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a gano sunanta ba.
Mazauna yankin sun gano gawarwakin daga baya inda suka kai su asibitin Guga inda aka yi musu sallar jana'iza kafin a binne su a safiyar Litinin, in ji rahoton Channels tv.

Source: Original
Rundunar yan sanda ta yi shiru
Wasu daga cikin mazauna garin sun nuna bacin ransu game da abin da suka bayyana da rashin halartar jami'an gwamnati da na tsaro yayin jana'izar.
Haka zalika, sun ce yankin Guga ya fuskanci hare-hare da dama a makwannin baya, inda aka samu mutuwar aƙalla mutane biyar kafin harin na ranar Lahadi.
Yayin da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa za su fitar sa cikakkun bayanai kan lamarin daga baya.
Sojoji sun ragargaji yan bindiga a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'addan da ke addabar mutane a jihar Katsina.
An ruwaito cewa dakarun runduna ta 17 ta sojojin Najeriya sun yi wa wasu da ake zargi ’yan ta’adda ne kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Dutsin-Ma ta jihar.
Yayin musayar wuta, sojojin sun yi nasarar hallaka yan bindiga guda uku tare da kwato mugayen makamai da kayayyakin da suke amfani da su.
Asali: Legit.ng

