An Gwabza Fada tsakanin Jami'an Tsaro da Ƴan Bindiga a Katsina, An Rasa Rayuka

An Gwabza Fada tsakanin Jami'an Tsaro da Ƴan Bindiga a Katsina, An Rasa Rayuka

  • Akalla jami'an CJTF hudu da farar hula daya sun mutu bayan artabu da 'yan bindiga a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina
  • Mazauna yankin Guga sun ce jajircewar CJTF da wasu masu aikin sa kai ta hana 'yan bindigan sace dabbobin al'umma
  • Rundunar 'yan sandan Katsina ta ce tana duba rahoton, yayin da gwamnatin jihar ba ta fitar da sanarwa ba tukuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Katsina – Akalla jami'an rundunar Civilian Joint Task Force (CJTF) hudu da farar hula daya sun rasa rayukansu bayan da ake zargin 'yan bindiga sun kai hari kauyen Guga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi lokacin da maharan suka kutsa cikin kauyen a kan babura da dama suna harbe-harbe domin razana mazauna yankin.

Kara karanta wannan

ADC ta kalubalanci Tinubu ya ziyarci Zamfara bayan mummunan hari

'Yan ta'adda sun hallaka jami'an CJTF a katsina
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta JTF a Monguno, jihar Borno. Hoto: JORIS BOLOMEY/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Yadda CJTF ta dakile harin 'yan bindiga

Mazauna yankin sun ce da isowarsu, 'yan bindigan sun nufi wurin da jami'an CJTF ke gadin kauyen, inda suka yi artabu mai tsanani da jami'an tsaro da masu gadin sa-kai, in ji rahoton Daily Trust.

Sai dai jajircewar jami'an CJTF da masu gadin sa-kai ta hana maharan cimma burinsu na sace dabbobin al'ummar kauyen, lamarin da ya tilasta musu janyewa ba tare da sun yi nasarar kwashe dabbobi ba.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya ce jami'an CJTF da suka mutu sun nuna matukar jarumtaka duk da cewa maharan sun fi su yawa.

Ya ce maharan sun shiga kauyen suna harbi ba kakkautawa, amma jami'an tsaron al'umma sun tsaya tsayin daka wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Yankin na fama da hare-haren 'yan bindiga

A cewarsa, sadaukarwar da jami'an suka yi ce ta hana 'yan bindigan sace dabbobi da kuma haddasa mummunar barna fiye da abin da ya faru.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban dan siyasa, matarsa da 'ya'yansa a Zamfara

Mazaunin ya bayyana cewa al'ummar Guga da wasu kauyukan arewacin Bakori sun dade suna fama da hare-haren 'yan bindiga, da suka hada da kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma satar dabbobi.

Ya kara da cewa al'umma na ci gaba da rayuwa cikin fargaba saboda yawaitar irin wadannan hare-hare, yana mai kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kara daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Wasu sassan Katsina na ci gaba da fama da matsalar tsaro.
Taswirar jihar Katsina, inda 'yan bindiga suka kashe 'yan CJTF da farar hula. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Abin da 'yan sanda suka ce

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gwamnatin jihar Katsina da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Sadiq Aliyu, ya shaida cewa rundunar tana tantance bayanan da suka shafi lamarin, yana mai alkawarin fitar da karin bayani idan bincike ya kammala.

Mutanen gari sun tari 'yan bindiga

A wani labari, mun ruwaito cewa, aƙalla mutane uku ne aka kashe lokacin da miyagu da ake zargi 'yan bindiga ne suka ƙaddamar da hare-hare a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kuma raunata mutane a hare-haren wadanda suka kai kan garuruwa dama a yankin karamar hukumar Malumfashi a daren ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026.

A cewar mazauna garin, hare-haren sun zo ne a matakai guda biyu, inda Gobirawa da Badole suka fi fuskantar tashe-tashen hankulan yayin da 'yan bindigar suka afka wa gidaje tare da buɗe wuta ba kakkautawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com