Bayan Abubakar Malami da Emefiele, Kotu ta Sake Karbe Dukiyoyin Janar a Soja
- Kotun ɗaukaka ƙara da ke Lagos ta tabbatar da hukuncin ƙwace dukiyoyin tsohon shugaban Operation Pulo Shield
- Janar Emmanuel Atewe (mai murabus) ya rasa N293.97m tare da kadarorin gidaje da filaye da hannun jari a kotu
- A hukuncin da kotun ta yanke na haɗin gwiwa, an yi watsi da ɗaukaka ƙarar da ya yi a shari’arsa da hukumar EFCC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Kotun daukaka kara ta tabbatar da karbe dukiyoyi, kadarori da kudi har N293.97m na wani tsohon janar a gidan soja.
A karshen shari’a, alkalai duka sun amince a karbe dukiyar Janar Emmanuel Atewe mai ritaya, a sallama su ga gwamnatin tarayya.
Premium Times ta rahoto cewa Mai shari’a Boloukuromo Ugo ya karanto shari’ar da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Legas.
Boloukuromo Ugo ya kori karar da Janar Atewe ya shigar, ya tabbatar da nasarar da babbar kotun tarayya ta ba hukumar EFCC.
Kotun daukaka karar ta yarda da hukuncin Chukwujekwu Aneke, ta ce ba a kawo hujjojin da za su sa a yi watsi da hukuncinsa ba.
Wasu kadarorin da Janar Emmanuel Atewe ya rasa
Cikin kudin da tsohon sojan ya rasa akwai kudi N293.97m da hannun jari na MTN 30, 000 a kamfanin IBTC Asset Management Ltd.
Sannan akwai tarin gidaje da filaye a birnin tarayya Abuja da kuma babban birnin jihar Bayelsa.
Wuraren da yake da filaye a Abuja sun hada da Jahi, Sabon Lugbe, Kuje, Gaube da Jahi, Sabon Lugbe, Kuje, Gaube sai fili a Yenagoa.
Ana zargin janar ya karkatar da kudin sojoji
Bayanai daga The Cable sun ce bincike ya gano yadda aka karkatar da kudin da aka ware wa Operation Pulo Shield domin aikin sojoji.
Jami’an EFCC sun ce an cire kudin zuwa wasu kamfanoni ba tare da an yi aikin fari ko na baki ba.
Wannan binciken ne kuma ya ci tsohon shugaban hukumar NIMASA, Patrick Akpobolokemi wanda kotu ta same shi da rashin gaskiya a 2023.
A binciken ne aka bankado yadda wasu kudi suka yi kafa daga kamfanin Cisco Nobots Limited, a karshe aka saye wani fili a Fatakwal.
Daga cikin wannan kudi an iya dawo da kaso mai tsoka. Duk da haka, wanda ake zargin ya fada wa kotu ba a same shi da laifi ba.
Duk uzurin da lauyansa ya bada, alkalai ba su karba ba don haka aka kori karar ta shi, ana cewa bai fadi ya mallaki wadannan dukiyoyi ba.
Tsohon shugaban NIMASA zai je kurkuku
Ana da labarin babbar kotun tarayya da ke Lagos ta yanke wa tsohon daraktan NIMASA, Kyaftin Ezekiel Bala Agaba, hukuncin dauri.
An yanke masa daurin shekaru bakwai a gidan yari kan sace N1.5bn. Shari'ar ta taba har da Patrick Akpobolokemi da Government Tompolo.
Kotun ta tabbatar da zargin lauyoyin hukumar EFCC cewa Agaba ya karkatar da wadannan kudi ne daga asusun hukumar zuwa amfanin kansa.
Asali: Legit.ng

