Amurka ta yi fallasa, ta fadi adadin 'ƴan Fulani' da ke ta'addanci a Najeriya

Amurka ta yi fallasa, ta fadi adadin 'ƴan Fulani' da ke ta'addanci a Najeriya

  • Hukumar USCIRF ta ce akwai kimanin Fulani masu ɗauke da makamai 30,000 da ke gudanar da hare-hare a Najeriya cikin ƙungiyoyi daban daban
  • Rahoton ya bayyana cewa hare-haren da ake dangantawa da mayaƙan Fulani sun haddasa dubban mace-mace da raba al’umma da matsugunansu
  • USCIRF ta zargi jami’an tsaro da jinkirin kai dauki yayin da kungiyar Miyetti Allah ta musanta hannu a duk wani tashin hankali da ake yi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Hukumar kula da ‘yancin addini ta Amurka (USCIRF) ta bayyana cewa akwai kimanin Fulani ɗauke da makamai 30,000 da ke ta'addanci a Najeriya cikin ƙungiyoyi daban daban masu mambobi daga mutum 10 zuwa 1,000.

Rahoton watan Mayun 2026 ya ce waɗannan mayaƙa sun zama daga cikin manyan masu haddasa take ‘yancin addini da kashe-kashe a Najeriya, musamman a yankin Middle Belt da wasu sassan Kudancin ƙasar.

Kara karanta wannan

Ranar Sallah: Ƴan sanda, NSCDC, FRSC sun dauki muhimman matakai na samar da tsaro

Hukumar Amurka ta ce Fulani masu dauke da makamai 30,000 ne ke ta'addanci a Najeriya
Wasu mutane sanye da kayan Fulani suna kallon ruwa. Hoto: Michael S. Lewis
Source: Getty Images

Hare-haren da Kiristoci ke fuskanta a Najeriya

Rahoton mai taken “Nonstate Violators of Religious Freedom in Nigeria: Fulani Militants” da aka wallafa a shafin USCIRF ya ce hare-haren da ake dangantawa da mayaƙan Fulani sun haddasa mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa al’ummomi barin gidajensu.

USCIRF ta bayyana cewa mafi yawan hare-haren sun fi shafar al’ummomin Kirista, duk da cewa Musulmai ma sun sha fama da kashe-kashe da garkuwa da mutane.

Rahoton ya ce:

“Hare-haren mayaƙan Fulani sun haddasa mafi yawan mace-mace tsakanin al’ummomin addini a Najeriya cikin shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da hare-haren sauran kungiyoyin ta’addanci.”

Rahoton ya kara da cewa mayaƙan kan kai hare-hare ne da dare ta amfani da babura, bindigogi masu sarrafa kansu da adduna domin razana jama’a da tilasta musu barin yankunansu.

An ambaci hare-hare a Benue da Plateau

Rahoton ya bayyana wasu hare-haren da suka faru a shekarar 2025 da farkon 2026, ciki har da kisan mutane sama da 200 a Benue da Plateau.

Kara karanta wannan

Adadin Musulman duniya da suka halarci aikin hajjin 2026 ya haura miliyan 1.7

USCIRF ta ce wani hari da aka kai Benue a watan Yunin 2025 ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 200 ciki har da ‘yan gudun hijira da ke zaune a wata cibiyar Katolika.

Haka kuma rahoton ya ce an kashe Kiristoci sama da 200 a Yelwata da ke Benue yayin da aka raba sama da mutum 3,000 da matsugunansu.

Rahoton ya ce wasu daga cikin hare-haren ana kai su ne da gangan a lokutan bukukuwan Kirista kamar Kirsimeti da Easter domin kara firgita mutane.

A cewar rahoton, a watan Fabrairun 2026 wasu da ake zargin mayaƙan Fulani ne sun kashe mutum 32 a jihar Neja tare da kai hari wata cocin Katolika a Kafanchan da ke Kaduna inda aka kashe mutum uku aka kuma sace wasu 11 ciki har da wani fasto.

Rahoton ya zargi gwamnati da gazawa

USCIRF ta ce jami’an tsaro na Najeriya kan yi jinkiri wajen kai dauki ga al’ummomin da aka kai wa hari, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Rahoton ya kuma ce wasu kungiyoyin Kirista suna zargin jami’an tsaro da nuna son kai ga wasu al’ummomin Musulmi yayin gudanar da bincike da ayyukan tsaro.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Kungiyar Fulani ta MACBAN ta usanta hannu a dukkan hare-haren da ake yi a Najeriya.
Wasu Fulani suna kiwo da tambarin MACBAN. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Miyetti Allah ta musanta hannu a rikicin

Rahoton ya ce an dade ana zargin kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN da kasa dakile hare-haren mayaƙan Fulani, amma kungiyar ta musanta goyon bayan duk wani laifi.

Kungiyar ta ce:

“Ba ma goyon baya ko daukar nauyin aikata laifi, tsattsauran ra’ayi ko tashin hankali ta kowace hanya.”

Rahoton ya ce gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin kasashen da ake zargi da take ‘yancin addini tun shekarar 2025, lamarin da ya sa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ayyana masu garkuwa da mutane da kungiyoyin mayaƙan Fulani a matsayin ‘yan ta’adda.

USCIRF ta ce duk da wasu matakan tsaro da sulhu da ake dauka, har yanzu rikicin na ci gaba a yankunan tsakiya na Najeriya.

Jagororin Fulani sun nemi a tattauna

A wania labari, mun ruwaito cewa, shugabannin Fulani a Zamfara sun koka kan yadda ake nuna musu wariya da zalunci, sun ce ba su duka ba ne ‘yan ta’adda ba.

Kara karanta wannan

An kashe mutum 8 bayan dan majalisa ya bada kyautar miliyoyin Naira a jihar Neja

A wani taron wayar da kai a Gusau, shugabannin Fulani sun bayyana damuwarsu, suka ce rashin adalci ke tura matasa shiga ta’addanci.

Wasu fitattun shugabannin miyagun ‘yan bindiga sun bayyana shirin su na mika wuya matukar gwamnati ta ba su tabbacin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com