ESN Ta Shirya Kai Hare Hare a Wasu Sassan Najeriya, DSS, Sojoji Sun Dauki Mataki
- Jami'an DSS da sojojin Najeriya sun cafke wasu kwamandojin ESN biyu da ake zargi da shirya hare-hare a Kudu maso Gabas
- Jami’an tsaron sun samu nasarar kwato makamai masu yawa ciki har da bindigogin AK-47 da na’urar harba rokoki a Enugu
- An gano cewa kungiyar ESN ta shirya amfani da kayan NYSC domin sojan gona yayin kai miyagun hare-hare da sace mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Enugu - Jami’an hukumar DSS tare da goyon bayan dakarun rundunar sojin Najeriya ta 82 Division sun dakile wani babban hari da kungiyar ESN ta shirya kaiwa a yankin Kudu maso Gabas.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa aikin ya samu nasara ne bayan bayanan sirri da DSS ta tattara wanda ya kai ga cafke wasu kwamandojin ESN biyu a yankin Garki da ke jihar Enugu a ranar Litinin.

Source: Twitter
ESN ta shirya kai hare hare a Kudu
Rahotannin da jaridar This Day ta samu sun nuna cewa wadanda aka kama sun shirya kai hare-hare kan shingen binciken jami’an tsaro tare da shirya garkuwa da mata, dalibai da yara a yankin.
Majiyoyin tsaron sun ce bayanan da aka samu daga hannun wadanda aka kama ne suka sa DSS neman taimakon rundunar soji ta 82 Division.
Daga nan aka kaddamar da wani samame na hadin gwiwa wanda ya kai ga gano ma'ajiyar makamai ta kungiyar ESN a yankin Agbani da ke jihar Enugu tsakanin ranar Talata da Laraba.
Makamai da jami’an tsaro suka kwato
A yayin samamen, jami’an tsaro sun kwato makamai da kayan yaki masu yawa daga maboyar kungiyar.
Kayayyakin da aka samu sun hada da na’urar harba rokoki guda daya, harsasan RPG guda biyu, bindigogin AK-47 guda 11 da harsasai sama da 1,000.
Haka kuma an kwato gidajen harsasai 18 na AK-47, gurneti, bindigar barkonon tsohuwa, sandar duka da wasu kayayyakin tsaro.

Source: Twitter
An gano kayan NYSC a maboyar ESN
Bincike ya kuma gano wando 10 na NYSC, riguna takwas da igiyoyin shaidar mutum guda hudu na masu yi wa kasa hidima.
Majiyoyi sun ce kungiyar ta shirya amfani da kayan ne domin sojan gona yayin kai hare-haren da suka shirya, in ji rahoton The Punch.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa kungiyar ta shirya kai hare-haren ne domin haddasa tsoro a jihohin Kudu maso Gabas da kuma rage amincewar jama’a ga jami’an tsaro.
Sun kara da cewa kungiyar na son nuna kamar yankin ya fada cikin mummunar matsalar tsaro.
Sojoji sun kashe 'yan IPOB/ESN
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojoji da ke aiki a Kudu maso Gabas sun kashe wasu mayakan Biyafra da kuma kungiyar tsaro ta Gabas (IPOB/ESN) guda biyar.
Hakazalika, takwarorinsu a Arewa maso Yamma, sun yi nasarar kubutar da mutane 15 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.
A yayin hare-haren sojojin, sun kwato tarin muggan makamai tare da kakkabe 'yan bindigar yayin da wasu suka ranta a na kare zuwa daji.
Asali: Legit.ng

