June 12: Tinubu Ya Fara da Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci, Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu

June 12: Tinubu Ya Fara da Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci, Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Najeriya yayin bikin ranar dimokuraɗiyya da ake yi a yau Juma'a
  • Tinubu ya gargadi 'yan bindiga da masu daukar nauyin ta'addanci su mika wuya ko su fuskanci hukunci mai tsanani
  • Ya ce an kashe sama da 'yan ta'adda 13,000 cikin shekara guda, yayin da sama da mutum 124,000 suka ajiye makamansu tun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa ba za a nuna jin kai ga masu haddasa ta'addanci da ke taimaka masu ba a Najeriya.

Tinubu ya bai wa 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu daukar nauyin ta'addanci wa'adi su mika wuya.

Tinubu ya gargadi masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yayin jawabi ga al'umma a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar yayin bikin Ranar Dimokuradiyya karo na 27 a jere da Najeriya ke yi, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Mutane sun huta, jami'an tsaro sun yi ajalin hatsabibin dan bindiga, Baccujo

Tinubu ya nuna damuwa kan tsaro

A cewarsa, duk da raguwar mace-macen da ke da alaka da ta'addanci da kashi 81 tun shekarar 2015, har yanzu akwai bakin ciki.

Ya ce bikin na wannan shekara ya samu cikas saboda ci gaba da tsare dalibai da malamai da aka sace a Oyo da Borno.

Ya ce:

"Ga 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu daukar nauyin ta'addanci: Ku mika wuya ko ku fuskanci karfin Najeriya.
"Ba za a ci gaba da bude kofar mika wuya har abada ba. Ba za a nuna jin kai ga masu zubar da jinin 'yan Najeriya ba."

Tinubu ya ce gwamnatin sa ta wuce matakin horaswa tare da kawayenta zuwa kai hare-haren da aka tsara daidai kan maboyar miyagu.

Ya bayyana cewa an raunana cibiyar jagorancin ISWAP da ke Arege a Borno ta hanyar hare-haren da aka kai.

Shugaban ya ce an kashe sama da 'yan ta'adda 13,000 cikin shekara guda da ta gabata, kamar yadda Daily Post ta ce.

Kara karanta wannan

Musulmai sun yi martani da ake alakanta addinin da ta'addanci da sace mutane

Sai dai ya jaddada cewa kofar gyaran hali tana nan a bude ga masu son ajiye makamansu.

Tinubu ya shawarci yan Najeriya kan haɗin kai
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yawan yan ta'adda da aka hallaka

A cewarsa, sama da mayaƙa da masu dogaro da su 124,000 sun ajiye makamansu tun shekarar 2023 ta shirin Operation Safe Corridor.

Tinubu ya ce ware Naira tiriliyan 5.41 a kasafin kudin 2026 domin tsaro alama ce ta kudurin kasa na murkushe ta'addanci.

Ya kuma bayyana cewa an amince da daukar sabbin jami'an 'yan sanda sama da 50,000 da dubban sababbin sojoji.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen rage gibin da ke tsakanin yawan jami'an tsaro da bukatun tsaron sama da mutum miliyan 230.

Tinubu ya amince cewa har yanzu damuwar tattalin arziki na addabar 'yan Najeriya duk da wasu nasarorin da aka samu.

Matawalle ya yabawa Tinubu kan tsaro

Mun ba ku labarin cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana kwarin gwiwa cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu karin kuri’un Arewa a 2027.

Ya ce ’yan adawa na yada furofaganda da labaran karya kan tsaro, suna yin watsi da ci gaban gwamnati wajen yaki da matsaloli masu.

Matawalle ya yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro kan kokarinsu,yana cewa dabarun Tinubu sun rage ayyukan ‘yan bindiga suna kawo zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.