Musulmai Sun Kosa da Mulkin Kirista, Sun Roki Gwamna Ya ba Musulmi Dama
- Kungiyar Musulmi a jihar Oyo ta kosa ta kalar mulkin da ake yi musamman duba da mabambantan addinai da ake da su a jihar
- Musulmin sun bukaci Gwamna Seyi Makinde ya nuna adalci da daidaito ta hanyar mara wa dan takarar Musulmi baya a zaben gwamnan PDP
- Kungiyar ta tuna yadda gwamnan ya nuna kusanci da Musulmi a baya, ciki har da gina masallaci da taimaka wa wasu a zuwa Hajji da Umrah
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Kungiyar Musulmin jihar Oyo mai suna MUSCOYS ta bukaci gwamnan jihar, Seyi Makinde ya tuna da su a zabe mai zuwa.
Kungiyar Musulmi ta bukaci da ya nuna soyayya da adalci ta hanyar goyon bayan dan takarar Musulmi a karkashin jam’iyyar PDP a zaben gwamna mai zuwa.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Ishaq Kunle Sanni ya sanya wa hannu wanda jaridar Tribune ta samu.
Yadda Makinde ya kusanci Musulmi a baya
Kungiyar ta tuna yadda Makinde ya nuna kusanci da Musulmai tun lokacin yakin neman zabensa wanda hakan ya tabbatar ba shi da matsala da su.
Ta ce gwamnan ya taba amincewa da yawan Musulmai a jihar tare da nuna musu goyon baya ta hanyoyi daban-daban masu ma’ana.
Daga cikin abubuwan da ta lissafo akwai gina masallaci a hedkwatar yakin neman zabensa da ke kan hanyar Iwo da kuma taimaka wa wasu Musulmai wajen gudanar da aikin Hajji da Umrah.
Sanarwar ta kuma ambaci sabon masallacin Adogba da aka gina bayan rushe tsohon wurin saboda aikin tashar mota ta zamani da gwamnatin jihar ta yi.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan mataki ya rage damuwar wasu da ke zargin gwamnatin Gwamna Makinde da rashin nuna kulawa ga addinin Musulunci.
Sai dai kungiyar ta nuna damuwa kan wasu kalamai da aka danganta da gwamnan yayin kaddamar da maniyyatan Hajjin bana inda aka ce ya nuna cewa ba lallai sai Musulmi ne zai gaje shi ba.

Source: Original
Musulmi sun nuna damuwa kan kalaman gwamna
A cewar kungiyar, irin wadannan kalamai suna tayar da hankali kuma suna iya rusa tsarin daidaito tsakanin Musulmi da Kiristoci wajen mulkin jihar.
Ta tuna yadda aka rika samun sauyin shugabanci tsakanin Kirista da Musulmi tun daga mulkin Adebayo Alao-Akala zuwa Abiola Ajimobi sannan zuwa gwamnatin Makinde.
Kungiyar ta ce kujerar gwamna ta fi tasiri da muhimmanci fiye da sauran mukamai kamar Sanata, saboda haka ya dace a kiyaye tsarin daidaito tsakanin addinai.
Punch ta ce MUSCOYS ta bukaci gwamnan da kada ya kawo tangarda ga tsarin adalci da zaman lafiya da ake da shi ta hanyar mara wa dan takarar Musulmi baya a PDP.
Kungiyar ta kara da cewa yin hakan zai kara tabbatar wa Musulmai cewa gwamnatin Makinde na tafiya da kowa ba tare da nuna wariya ba.
A karshe, kungiyar ta yi addu’ar Allah ya ci gaba da ba jihar Oyo da Najeriya baki daya zaman lafiya da ci gaba.
Salla: Gwamna ya gargadi masu sayar da dabbobi
A wani labarin, an ji cewa gwamnatin Oyo ta tura gargadi mai zafi ga mazauna jihar da masu sayar da dabbobi da suka hada da shanu da raguna a titi.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kafa doka domin tabbatar da samun tsaro yayin da ake shirin bukukuwan salla babba.
Mahukunta da masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa dokar hana kiwo a bude ba ta da nufin tauye wata kabila.
Asali: Legit.ng


