Dakarun 'Yan Sanda Sun Kutsa Dajin Zamfara, Sun Yi Gaba da Gaba da 'Yan Bindiga

Dakarun 'Yan Sanda Sun Kutsa Dajin Zamfara, Sun Yi Gaba da Gaba da 'Yan Bindiga

  • Dakarun rundunar yan sanda sun karbe iko da dajin Jangebe da ke jihar Zamfara bayan artabu da miyagun 'yan bindiga
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, ya ce jami'an tsaron sun yi nasarar hallaka yan bindiga uku a musayar wuta
  • Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai farmaki a maboyar ‘yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta samu gagarumar nasara a yaki da ta'addanci, bayan ta kashe wasu ‘yan bindiga uku a wani farmaki da ta kai cikin dajin Jangebe.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ya fitar a Gusau.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

Yan sanda.
Dakarun yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Ya ce an gudanar da aikin ne bayan tura motocin sulke (APCs) da kuma motocin CSK da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin inganta sintiri a dazuka da yankunan da ‘yan bindiga ke fakewa, cewar rahoton Leadership.

Yan sanda sun kutsa dajin Jangebe

A cewar sanarwar, a ranar 7 ga watan Yuni, 2026 da misalin karfe 6:00 na yamma, rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta kai farmaki a mafakar yan bindiga a kauyukan Taza, Wuya da Gwaram da ke dajin Jangebe a karamar hukumar Anka.

Rundunar ta kunshi jami’an sashen yaki da manyan laifuffuka na tashin hankali (VCRU), rundunar ‘yan sanda ta Zamfara da kuma ‘yan sa-kai na Civil Security Volunteers.

Rahoton Daily Post ya nuna cewa farmakin ya samu jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello.

An gwabza kazamin fada da ‘yan bindiga

Sanarwar ta bayyana cewa da isar jami’an tsaro yankin, sun fuskanci ‘yan bindiga dauke da mugayen makamai, lamarin da ya kai ga musayar wuta mai tsanani.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara ɗaukar mataki kan rashin tsaro, ana son samar da yan sandan jihohi

A karshe, jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga uku, yayin da wasu da dama suka tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga. An kuma kama mutum daya da ake zargi.

Rundunar ta ce an kwato kayayyaki da makamai da suka hada da bindigogi AK-47 guda uku, harsasai 23, magazines uku da kuma babura 10.

Ta kuma ce babu wani jami’in ‘yan sanda ko na sauran rundunonin tsaro da ya rasa ransa ko ya jikkata a farmakin.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda za su kara kaimi

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa wannan farmaki na da matukar muhimmanci, domin shi ne karon farko da aka shiga kai tsaye cikin wannan bangare na dajin Jangebe da ake gani a matsayin mafakar ‘yan bindiga mai hadari.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai farmaki a maboyar ‘yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya.

Yan bindiga sun sace dattawa 50

A wani rahoton, kun ji cewa miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dattawa 50 da suka daji domin zaman sulhu a yankin karamar hukumar Maradun a Zamfara.

Kara karanta wannan

An fara jita jitar cewa Sheikh Abdulmudallib ya samu tikitin takarar gwamna a 2027

Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da dattawan ne bayan sun je tattaunawar sulhu da jagoran daya daga cikin dabar ‘yan bindiga mai suna Jammo.

Bayanai sun nuna cewa an sako mutum 11 daga ciki, yayin da har yanzu mutum 39 ke hannun masu garkuwa da mutanen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262