Rai Bakon Duniya: Shugaban Izala a Kebbi Ya Rasa Ransa a hannun ’Yan Bindiga
- An sanar da rasuwar Malam Yahaya Billi, shugaban Izala na Besse, bayan ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane
- Sanarwar ta jaddada cewa kowane mutum yana da hanyar da Allah Ya ƙaddara zai karɓi rayuwarsa a duniya
- An bukaci al'umma su halarci Sallar Ga'ib da za a gudanar a Garkan Sarki da misalin ƙarfe 4:30 na yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Besse, Kebbi - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wani daga cikin wadanda yan bindiga suka sace a Kebbi ya rasa ransa.
An tabbatar da mutuwar shugaban kungiyar Izala a Besse da ke jihar Kebbi bayan shafe kwanaki a hannun yan bindiga a daji.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne mai tayar da hankali daga shafin Abdullahin Gwandu TV a Facebook da ke yada karatuttukan malaman Musulunci.
Yadda marigayin ya rasu a hannun ƴan bindiga
Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya rasu ne a hannun ƴan bindiga a ranar Litinin 8 ga watan Yunin 2026 da muke ciki.
Wannan lamari ya jefa iyalai, abokai da al'ummar Besse cikin jimami da alhini sakamakon wannan babban rashi.
Biyo bayan rasuwar tasa, an sanar da gudanar da Sallar 'Ga'ib' domin yi masa addu'a da neman rahamar Allah.
Yaushe za a gudanar da sallar jana'izar marigayin
Za a gudanar da Sallar Ga'ib din ne a wurin da ake kira Garkan Sarki domin bai wa jama'a damar halarta.
An tsara lokacin gudanar da sallar da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar yau Talata 9 ga watan Yunin shekarar 2026 da muke ciki.
Sanarwar ta fito ne daga ƙungiyar JIBWIS Besse Media Team domin sanar da jama'a wannan babban rashi.
Sanarwar ta ce:
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
"Kowane mutum yana da irin hanyar da Allah Madaukakin Sarki Ya ƙaddara zai karɓi rayuwarsa.
"Allahu Akbar, Allahu Akbar. Allah ya yi wa Malam Yahaya Billi, Shugaban Izala na Besse, rasuwa a hannun masu garkuwa da mutane a ranar jiya."
Saboda haka, sanarwar ta tabbatar da cewa za a gudanar da Sallar Ga'ib a yau Talata kamar haka:
- Wuri: Garkan Sarki.
- Lokaci: Ƙarfe 4:30 na yamma.

Source: Original
Rokon da aka yiwa al'umma game da jana'izar
An bukaci al'umma da masoya marigayin su halarta tare da yin addu'ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa.
Haka kuma, an roƙi Allah Madaukakin Sarki ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi tare da bayinsa nagari.
Yan bindiga: Tsohon Janar ya roki gwamnati
Mun ba ku labarin cewa yan bindiga sun fitar da sabon bidiyon tsohon Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya da matarsa da aka sace.
Masu garkuwar sun bukaci a sako wasu mutane uku da suke tsare tare da mayar musu da dabbobin da suka ce an kwace.
Janar din mai ritaya ya yi kira ga zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha'awar tattaunawa da zaman tare cikin lumana.
Asali: Legit.ng

