Hukumar Kwastam ta kama kaya na miliyan N41.4 a jihar Kano
- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama buhu 707 na shinkafar waje da aka yi fasakwaurin ta a Jihar Kano
- Ofishin Hukumar reshen Jigawa da Kano ya ce sun kwace shinkafar ne tare da wasu kayayyakin da aka yi fasakwaurinsu
- Kimar kudaden kayan da suka kama ta kai Naira miliyan 41.3 daga watan Yuli zuwa Satumba
Hukumar kwastam ta kwace haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan 41.4 a jihar Kano da Jigawa a cikin watanni ukun da suka gabata.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kwanturolan hukumar na shiyar Kano da Jigawa, Suleiman Pai Umar, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba.
Rabe-raben abubuwan da aka kwace sun haɗa da: buhuhunan shinkafa yar waje 707 wadanda kimar kudadensu ya kai N20.5 miliyan, dila 155 na kayan gwanjo na N11.6 miliyan, jarkoki 625,16 na man girki kan N334,000, kwalayen taliya 130 na N1.95 miliyan, kwalayen madara 231 na N5.08 miliyan da kwalin macaroni takwas na N104,000.
Sauran abubuwan da aka kama sun hada da: kwali 30 na maganin sauro na hayaki na N660,000, katan 29 na Couscous da kudinsa kai N337,000, katan 10 na batir na N220,000, katon shida na angur da aka sarrafa a kasar Ghana na N308,000 da katan 85 na magungunan da ba a yi wa rajista ba.
Umar ya nuna damuwa cewa har yanzu wasu ‘yan Najeriya na ci gaba da yin fasa kwauri duk da sanin barazanar fasa-kwaurin ga lamarin tsaro da tattalin arzikin ƙasar, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce:
“Kamen wani bangare ne na ayyukanmu na hana fasa kwauri tun daga watan Yuli. Yana da ban tsoro cewa har yanzu wasu ‘yan Najeriya na ci gaba da yin fasa kwauri, duk kuwa da yawan sanin barazanar fasa kwauri ga tsaro da tattalin arzikin kasar.”
Kwastam za ta fara amfani da 'Drone' wajen sintiri da kama haramtattun kayayyaki
A wani labarin, Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), ta ce nan ba da jimawa ba za ta tura jirage marasa matuka a Seme don yin sintiri mai inganci wajen duba ayyukan fasa kwabri a yankin kan iyaka, Daily Nigerian ta ruwaito.
Kodinetar Yanki na NCS, Modupe Aremu, Mataimakiyar Kwanturola Janar (ACG) na Kwastam, ta bayyana hakan a ranar Litinin 20 ga watan Satumba yayin ziyarar aiki zuwa Kwamitin Yankin Iyakokin Seme.
A cewarta, za a yi aikin kula da iyakokin ta hanyar zamani da amfani da jirage marasa matuka don tabbatar da cewa za a iya nazarin yankin game da abin da ke faruwa.
Asali: Legit.ng