‘Za Ku Dandana Kudarku’: Trump Ya Nuna Yatsa ga Rasha da China game da Iran
- Shugaba Donald Trump ya gargadi Rasha da China game da taimaka wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Iran ta ce ba za ta mika kai ga barazana ko matsin lambar Amurka ba, tana jaddada kare muradunta a mashigin Hormuz kafin tsagaita wuta
- Oman ta ci gaba da shiga tsakanin Iran da sauran ɓangarori domin cimma yarjejeniya kan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump ya gargadi Rasha da China yayin da ake ci gaba da yaki da Iran.
Trump ya bayyana cewa za su fuskanci sakamako mai tsanani idan suka bai wa Iran makamai ko taimaka mata ta wannan hanya.

Source: Getty Images
Trump ya gana da shugabannin China, Rasha
Trump ya ce Shugaban China Xi Jinping ya tabbatar masa a ganawarsu da aka yi a Beijing cewa China ba za ta sayar wa Iran makamai ba, cewar Al Jazeera.
Ya kuma bayyana cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba shi irin wannan tabbaci duk da ci gaba da yaƙin Ukraine, yana cewa Moscow ba za ta bai wa Tehran makamai ba.
Trump ya rubuta cewa idan ɗaya daga cikin waɗannan manyan ƙasashe ya karya wannan alkawari, hakan ba zai kasance cikin muradunsu ba kuma zai haifar da mummunan sakamako.
Iran na tattaunawa da Rasha, China
Kalaman shugaban Amurka sun zo ne yayin da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya gana da takwarorinsa na China da Rasha a taron SCO da aka gudanar a Kyrgyzstan.
Bayan taron, Araghchi ya bayyana cewa Iran ba za ta mika kai ga barazana, matsin lamba ko tsoratarwar Amurka ba, kuma za ta ci gaba da kare muradun ƙasarta.
Ya ce kare al'ummar Iran da kuma muradun ƙasar a mashigin Hormuz na daga cikin manyan manufofin gwamnatin Tehran da ba za ta yi watsi da su ba.

Source: Getty Images
Araghchi ya ƙara da cewa Iran na ci gaba da tattaunawa da Rasha, China da Pakistan kan hanyoyin kawo ƙarshen rikicin da ake fama da shi.
Ya jaddada cewa Tehran ba za ta tattauna batun tsagaita wuta ba har sai an cimma halastattun buƙatun al'ummar Iran dangane da mashigin Hormuz, cewar Reuters.
A halin yanzu, rikicin yankin ya ci gaba da tsananta bayan Trump ya sanar a ranar 8 ga Yuli cewa yarjejeniyar tsagaita wutar Islamabad ba ta ƙara aiki.
Tun daga wannan lokaci, Amurka da Iran sun yi musayar hare-hare, inda Washington ta kai farmaki kan wasu wurare a Iran, yayin da Tehran ta ce ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojin Amurka.
Tawagar Oman ta isa Tehran
A wani yunƙurin sasanta rikicin, tawagar Oman ta isa Tehran domin tattaunawa da jami'an Iran kan yadda za a tsara zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz.
Rahotanni sun ce Oman da Iran sun riga sun kafa kwamitin haɗin gwiwa domin neman mafita, sai dai har yanzu ba su cimma cikakkiyar yarjejeniya kan tsarin ba.
China ta gargadi Amurka kan haraji
Mun ba ku labarin cewa kasar China ta soki sababbin harajin da Amurka ta ƙaƙaba kan kayayyakinta da na wasu ƙasashe 59.
Amurka ta ce harajin ya danganci hana shigo da kayayyakin da ake zargin an samar da su ta hanyar aikin dole.
Beijing ta ce za ta ci gaba da aiki da Amurka wajen rage takaddamar haraji, amma matakan na iya sake jawo da matsala.
Asali: Legit.ng

